Home / Labarai / Ci Gaban Najeriya Sai An Daina Shigowa Da Kayayyakin Waje  – ACF

Ci Gaban Najeriya Sai An Daina Shigowa Da Kayayyakin Waje  – ACF

Mustapha Imrana Abdullahi
Kungiyar tuntuba ta arewacin Najeriya (ACF) ta bayyana cewa indai ana bukatar kasar ta samu ci gaban da ake bukata sai an yi taka tsan tsan wajen shigowa da kaya a cikin kasar.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin takardar bayan taron da ta fitar a karshen taron shugabannin majalisar kolin kungiyar da suka fito daga Jihohin arewa Goma sha Tara da aka yi a babban dakin taron hedikwatar kungiyar da ke Kaduna.
Da yake karantawa manema labarai bayanin irin abubuwan da suka cimma a taron shugaban kungiyar tuntuba ta arewa Chief Audu Ogbeh ya ce hakika dole ne ayi taka- tsan- tsan wajen batun shigowa da kayayyaki cikin tarayyar Najeriya domin kasar ta samu nasarar da ake bukata.
” A kokarta wajen fitar da kaya kasashen waje daga Najeriya a madadin shigowa da kayayyaki cikin kasar, saboda irin yadda a yanzu kudin kasashen waje musamman yadda Dala take a matsayin kudin Najeriya abin dubawa ne in har ana son mu ciyar da kan mu gaba”, inji shi.
Ya kara da cewa irin yadda ake shigowa da Madara cikin tarayyar Najeriya na bayar da kashi shida (6) na yawan abin da ake samu a tattalin arzikin kasar, wanda hakan abin duba wa ne kwarai.
“Najeriya na kashe makudan kudin da suka kai dala miliyan daya da digo shida ($1.6) wajen shigowa da Madara da ake yin amfani da ita cikin kasar, wanda shi ma abin duba wa ne kwarai.
Taron na kungiyar ACF ya kuma yaba tare da yi wa Gwamnonin Borno da Kebbi, wato Farfesa Babagana Umara Zulum na Jihar Borno da kuma takwaransa na Jihar Kebbi Alhaji Abubakar Atiku Bagudu bisa yadda suke kokari wajen tunkarar batutuwan matsalar tsaro a Jihohinsu wanda sakamakon hakan muke yin kira ga sauran Gwamnoni su yi ko yi da abin da suke yi.
Taron karkashin Chief Audu Ogbeh ya kuma yi kira ga daukacin Bankuna da su hanzarta yin duba game da irin kudin ruwan da suke karba ga duk wanda ya ke son bashi daga wurinsu, saboda babu yadda za a yi mutum ya iya gudanar da wata sana’a idan za a karbi kashi 25 na kudin ruwa daga bashin da ya karba domin gudanar da sana’a wanda hakan na yi wa tattalin arzikin kasa babban nakasa don haka ACF na yin kira ga Gwamnati da dukkan hukumomin da abin ya shafa su hanzarta kawo Gyara.
Saboda sai an samar da aikin yi ga daukacin matasa kafin kasa ta samu nasarar ci gaban da kowa ke bukata, amma tsarin da Bankuna ke tafiya a kansa na kudin ruwa ga masu neman bashi domin sana’a ko masana’antu ba abin da yake haifarwa sai durkushewar sana’o’i da masana’antun kawai.
Haka nana ma batun matsalar tsaro na haifar da durkushewar kasuwanci da masana’antu tare da harkar Noma duk da yankin Arewa na da kashi 75 na yawan kasa wanda hakan ya ba yankin ikon Noma abin da zai wadaci nahiyar Afrika baki daya.
Har ila yau ACF ta kuma yabawa jami’a taron Najeriya a kan irin yadda suke sadaukar da rayuwarsu wajen kokarin tabbatar da tsaro.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.