Home / MUKALA / MATSALAR YAN BINDIGA: TARIHI YA NUNA AMFANI DA KARFI SHI NE MAFITA

MATSALAR YAN BINDIGA: TARIHI YA NUNA AMFANI DA KARFI SHI NE MAFITA

Abu Humaida Abubakar Abdullahi Akwa

 

A ‘yan kwanakin nan an samu tabarbarewar tsaro a yankin Arewa maso yammacin Nijeriya sakamakon ayyukan yan bindiga da ke kashewa da yin garkuwa da mutane. Gwamnati na iya kokarinta don ganin cewa an magance matsalar sai dai tana fuskantar kalubale daga wasu bangarori na alumma wadanda suke ganin sulhu shine mafita.
Sai dai tarihi ya nuna mafi yawan matsalolin tsaro da suka danganci amfani da makami ana magancesune kawai ta amfani da makami. Hakan zai tilastawa masu rike da makamin su nemi mafaka ko afuwa. Misali a daular farko ta musulunci wato Daular Umawiyya (661 -750 CE) an sami matsalolin tsaro da dama wanda aka yi amfani da makami wajen murkushesu. Kamar boren Al-ash-ath ( Abdurahman dan Muhammad dan Al-ash-ath), boren Al-ash-daq (Abu Umayya Amr dan Said Al-ash-daq) da  boren Yazid dan Mahallab. Sannan akwai boren Al-Harith dan Suraij Almarji’I da boren Zaid dan Ali dan Hussein da dai sauransu.
Shi dai boren Al-ash-ath  ya farune a zamanin Kalifa Abdulmalik dan Marwan dan Hakam a kasar Iraq karkashin gwamna Hajjaju dan Yusuf . Duk da yake Kalifa yaso ayi sulhu kamar yadda wasu ke kira a Nijeriya amma bai yiwu ba sai da aka ba hammata iska aka kashe da yawan cikin yan tawayen. Shi kuma Al-ash-ath ya jagoranci ragowar magoya bayansa zuwa Khorasan don neman mafaka a wurin wani sarki Zunbil. Daga baya dai masana tarihi sun nuna sarkin yaki mikashi ga Hajjaju inda ya sare kansa. Dukkan sauran boren hakan aka bi wajen murkushe mabiya ta inda daga baya akan kama shugaban a kasheshi in banda boren Zaid dan Ali.
Boren Zaid dan Ali ya sha banban domin shi mafi yawan magoya bayansa sun mika wuya ta inda ragowar aka yakesu  a fagen fama, shima ya rasa rayuwarsa ta hanyar harbinsa d kibiya a goshi a lokacin Kalifa Hisham dan Abdulmalik. An binne gawarsa a Kufa sai dai daga baya an hako gawar tasa aka tsireta har shekara uku don ta zama darasi ga masu son yiwa hukuma bore. Daga baya aka konata aka zuba tokar a kogin Furata na Iraqi. Bayan faduwar Daular Umawiyya,  Sarakunan Abbasiyya suka samu mulki suma sun hako gawar Hisham suka konata suka zuba tokar a ruwa don ramako.
Irin wannan hanya ta amfani da karfin makami tayi tasiri sosai a tarihi wajen samar da tsaro da tsoratar da yan a fasa kowa ya rasa. An yi haka a dauloli da kasashe daban daban a tarihi da kuma a yau. Sai dai na takaita misali kan daukar umawiyya ne saboda alakarta da musulunci wanda yake da tasiri a Arewa maso yammacin Nigeria. Allah ya datar damu. Ameen.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.