Home / Labarai / Na Ga Abin Tausayi, Ban Haushi Da Takaici – Nasiru El-rufa’i

Na Ga Abin Tausayi, Ban Haushi Da Takaici – Nasiru El-rufa’i

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i, ya bayyana cewa a ziyarar da ya kai wuraren da aka kaiwa wadansu garuruwa a karamar hukumar Giwa inda yan Ta’adda suka Konawa mutane gidaje,Amfanin Gona da kuma kashe jama’a ya ga abin haushi da takaici sakamakon irin abin tausayin da ya gani na yadda mata, yara suka tagayyara.
Malam Nasiru ya ce ya kai ziyarar gani da idanunsa inda aka kone wa mutane amfanin Gona da gidaje kuma “mun kai ziyara a garin Fatika da Zariya inda jama’ar da aka kaiwa harin ke gudun hijira.
“Garin Fatika ne babban gari a kauyukan da aka kaiwa harin don haka suka je garin domin hijira wasu kuma sun wuce Zariya domin tsira da ransu da yayansu, na ga abin tausayi, ban haushi da takaici sakamakon irin yadda mutane da suka hada da kananan yara suke cikin wani mawuyacin hali bayan da suka bar gidajensu, sakamakon harin da aka kai wa garuruwansu”, inji Gwamna
Ya kara da cewa a gobe zai je ya ga shugaban kasa kuma zai fayyace masa abin da ya faru kuma ya nemi taimakon Gwamnatin tarayya domin a taimakawa mutanen nan”.
Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufa’I ya ci gaba da cewa za su taimakawa wadannan mutane kuma za a gina garuruwan da abin ya shafa kuma zai nemi taimakon yan kasuwa da duk wani mai halin da zai iya taimakawa domin a taimakawa wadannan mutane.
Na kuma bayar da umarni ga shugaban karamar hukumar Giwa da a tantance irin Barnar da aka yi da wadanda abin ya shafa kuma za mu taimaka ta hanyar hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kaduna domin mutanen da abin ya shafa su samu sauki”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.