MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC Dokta Abdulkadir Durunguwa ya bayyana cewa burinsa shi ne samar da dauwamammen zaman lafiya a Jihar Kaduna.
Abdulmalik Duringuwa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen bude bakin da ya shiryawa yan jarida da aka yi a cibiyar yan jarida ta kasa reshen Jihar Kaduna.
Durunguwa ya ce akwai wani abu da wasu ba su Sani ba shi ne ko shugabanni kansu su na matukar jin tsaro a yanayin rashin tsaro.
“Don haka babban buri na shi ne in samar da tsaron lafiya da dukiyar al’umma idan Allah ya ba ni mulkin Jihar Kaduna”.
Ya ci gaba da cewa ” duk a cikin yan siyasar da ke neman wannan shugabancin Jihar Kaduna babu wanda ya fi ni sanin ciki da wajen Jihar, domin babu wani sako da lungun da ban Sani ba a Jihar”, inji Duringuwa.
“Ina yin siyasa tun a shekarar 1982 zamanin siyasar Shagari muna cikin jam’iyyar NPN don haka ina da masaniyar siyasa sosai fiye da sanin wadansu mutane”.
“Kuma.wani lamarin da zan tabbatar idan na zama Gwamnan Jihar Kaduna shi ne tare da al’umma za a samar da ingantaccen tsarin tsaro da zai amfani kowa”.
Haka zalika “idan yankunan karkara sun samu ingantattun asibiti, wadatacciyar wutar lantarki,hanyoyi masu kyau da ingantar harkar Noma babu wanda zai zo cikin Birni har ya kai ga zama a wurin kowa zai zauna a inda yake domin ya samu komai a wadace”. kamar yadda Duringuwa ya tabbatar.
Saboda ni buri na shi ne samar da ingantacciyar Jihar Kaduna da kowa zai ji dadin ta a koda yaushe, domin haka da zarar na samu mulki a shirye nake in yi aikin da kowa zai ce Allah sam barka sakamakon farin cikin da mutane suka samu kansu a ciki.
Sai dai Abdulmalik Duringuwa ya yi kira ga manema labarai da su bayar da rahoton kowa ne dan takara da yazo ko ya nemi su isar da sakonsa ga jama’a.
Ya kuma ce ” hakika yankunan karkara na matukar bukatar a kula da su ta fuskar aiki da sauran abubuwan more rayuwa, ni na fito daga kauyen Ladduga ne a karamar hukumar Kachiya, kuma ina alfahari da hakan”.
Abdulmalik Durunguwa wanda kwamishina na na Gwamnatin tarayya a hukumar Kidayar jama’a ta kasa mai kula da shiyya ya fadakar da daukacin al’umma game da bukatar da ke akwai na kula wa da yawan jama’a domin samun damar daukar nauyinsu.
“Saboda duk shugaban da bai kula da wannan tsarin na yawan jama’a ba to, zai zamo kawai ana dai yi ne kawai kamar abin da ake cewa ana tukkar gaba baya na warwarewa wanda hakan ba al’kairi ba ne ta fuskar ci gaban kasa, mutane su dawo daga irin tunanin nan na in auri mace kawai ta ci gaba da haihuwa ba tare da tunanin yadda za a rike yayan ba, domin ni na sha Gwagwarmayar rayuwa fiye da tunanin jama’a don har yaron mota na yi da dai sauran fadi tashi da damar gaske har inda Allah ya kai ni a yanzu”, inji Duringuwa.
Sai ya yi kira ga jama’a da su rika sawa a ransu cewa da ikon Allah duk abin da suke tunani a duniya mai yuwuwa ne.
Ya ce dalibansa da ya koyawa darasin lisaafi a matakin makarantar Sakandare duk a yanzu sun shigo cikin wannan yunkurin nasa na zama Gwamnan Jihar Kaduna domin wasu a cikinsu manajoji ne a wuraren ayyuka daban daban wasu kuma sun samu matsayi babba a wuraren da suke yin aiki sun kuma ce idan da ban da na Koyar da su ilimin lissafi ba da yaya za a yi su iya kaiwa a halin yanzu wuraren da suke, wannan abin farin ciki ne kwarai a gare ni da sauran al’ummar Jihar Kaduna.