Home / Labarai / A Bari Jama’a Su Mallaki Bindigu Irin AK 47, RPG – Dikko Radda

A Bari Jama’a Su Mallaki Bindigu Irin AK 47, RPG – Dikko Radda

An yi kira ga Gwamnatin Najeriya da ta bari yan kasar su mallaki bindigu domin su kare kawunansu daga yan bindiga masu sata da kisan jama’a ba gaira ba dalili

Wannan tunani da kira ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Katsina Dokta Dikko Umar Radda a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Abuja babban birnin tarayyar kasar.

Inda ya fadakar da duniya kan cewa in har yan bindiga masu tashin tashina za su samu damar mallakar bindigu don haka ya dace a bari sauran jama’a su mallaki nasu bindigun.

“Idan har yan bindiga za su je kasuwa kuma su sayi bindiga kamar AK – 47. Da bindigar RPG, to sauran jama’a fa da ke bukatar su kare kansu? Saboda haka a bar su duk kowa ya mallaki bindigarsu.

“Wadannan mutanen yan bindigar na mallakar ne ba bisa ka’ida ba, don haka muna kokarin mallakar bindigar ne ta hanyar da ta dace, me zai hana a bari mutane duk su mallaki bindigar domin su kare kansu daga kalubalen da ke fuskantarsu”.

Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya tabbatar da cewa batun tattaunawa da yan Ta’adda masu dauke da bindiga ba abune mai yuwuw a ba a halin yanzu a nawa tunanin

Amma kuma idan su masu dauke da bindiga ba bisa ka’ida ba sun fito suka ce

“Mun ajiye makaman mu, don haka bari mu zauna domin mu tattauna, zamu yi kokarin mayar da su cikin al’umma”, inji Dikko Radda.

Ya ci gaba da cewa: “Mu Gwamnaoni da ake kiran mu shugabannin tsaro  da baki kawai a Jihohi, amma ba mu da ikon bayar da umarni ga sojoji, Yan Sanda ko jami’an tsaron farin kaya na sibil defens, duk suna karbar umarni ne daga can sama.

“A kokarin da muke yi, mun samar da wani bangaren samar da bayanan sirri daga jami’an tsaron da ke cikin al’umma a Jihar Katsina.

Kuma jami’ai ne na boye da ko su ba su ma san su ba sam, kuma dalilin samar da su shi ne domin mu tabbatar da an yi aiki sosai da kuma samar da bayanan sirri.

About andiya

Check Also

Return Our Property, Documents In Your Possession, SWAN Tells Ex-President Sirawo

    The Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) has warned its erstwhile National President, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.