…ranar 3 ga watan Disamba ce ranar kulawa da masu nakasa
Daga Imrana Abdullahi
Wani bawan Allah mai fama da nakasar gani da ke da bukata ta musamman da zaune a cikin garin Kaduna Mista Dokta Micah, ya bayyana bukatar da ake da ita a duk fadin duniya a kan taimakawa mutane masu bukata ta musamman a fannonin harkokin rayuwa daban daban.
Dokta Micah Shabi ya ce suna yin kira ga daukacin al’ummar kasa da duniya baki daya da su hanzarta taimakawa daukacin al’umma a fannoni daban daban na rayuwa da suka hada da harkokin Ilimi, Lafiya, Noma da samar wa da masu fama da nakasa ingantaccen kyakkyawan muhalli da nufin samun rayuwarsu ta inganta.
A ceto masu fama da nakasa da ke kan tituna suna yin barace – barace domin samun al’umma ta gari da kasa tare da duniya za su yi alfahari da ita a nan gaba.
Indai za a iya tunawa a duk ranar 3 ga watan Disamba na kowace shekara ne ake yin taron gangamin fadakarwa da nufin Ceto masu fama da nakasa a fannonin rayuwa da suke tattare da su a duniya.
A wannan shekarar dai ana saran samun halartar masu fama da nakasa a kalla mutum dari a dakin taro na gidan tunawa da marigayi Sardauna Ahmadu Bello da ke cikin garin Kaduna
A wata tattaunawar da wakilin mu ya yi da wasu daga cikin masu fama da nakasa sun bayyana masa irin wasu daga cikin halin da suke ciki na rayuwa da babu dadin ji ko gani da idanu