Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban kwamitin aikin Gona na majalisar wakilai ta kasa Honarabul Muktar Dandutse, mai wakiltar kananan hukumomin Fintuwa da Dandume, ya yi kira ga daukacin yan Najeriya da su daina yamutsa batun tsaro da siyasa domin masu yin hakan ba su wata kasar da ta wuce Najeriya.
Honarabul Muktar Dandutse ya bayyana hakan ne a lokacin wata tattaunawa da gidan Talbijin na NTA cikin shirin da ake yi a ranar Talata “Tuesday Live” a shirin tattaunawa yadda za a bunkasa harkar Noma.
Honarabul Dandutse ya ce duk mai son yin siyasa ya dace ya mayar da hankali wajen neman kuri’un jama’a ba hargitsa lamarin tsaro da siyasa ba domin neman biyan bukata a saukake.
Dandutse ya ci gaba da cewa Najeriya kasa ce da Allah ya yi wa dimbin albarka ta Noma da albarkatun kasa don haka idan an mayar da hankali wajen aikinta albarkar da Allah ya bayar za a samu ci gaba kwarai
Ya kara da cewa batun yamutsa kabilanci, siyasa da harkar tsaro ba zai kai kasar nan ta tudunmuntsira ba saboda kamar yadda ya bayar da misali da garinsa na Funtuwa a karamar hukumar Funtuwa da ya ce kashi Talatin na mutanen ta al’ummar Yarbawa ne kuma kashi Ashirin yan kabilar Igbo ne kuma duk ba za su iya gano asalin garuruwan iyayensu ba don haka ta yaya za a iya ce masu su tashi ko wani abu mai kama da hakan domin kawai ana son yin siyasa, saboda haka kowa ya bude idanunsa.
Sakamakon matsalolin tsaro irin na yan bindiga da masu satar mutane dai a binciken da wakilin mu ya yi ya gano cewa harkar Noma na cikin wata matsala da musamman da Honarabul Muktar Dandutse ya ce na bukatar daukar matakan gaggawa.
Wakilin kananan hukumomin Funtuwa da Dandume honarabul Dandutse ya kuma yi kira ga yan jarida da su dage wajen kokarin bunkasa kasa ba kokarin yin aiki sabanin na bunkasa kasa tare da al’ummarta ba.