….Halin da Ake ciki fa Koma WA baya ne- Jidadi
Daga Imrana Abdulllahi
Alhaji Aminu Surajo Funtuwa, shugaban kungiyar masu sana’ar Hatsi karkashin Amana Farms and Greens supply of Nigeria, ya yi Kira ga Gwannatin tarayya karkashin jagirancin Bola Ahmad Tinubu da ta hanzarta duba wa domin yin Gyaran da ya dace a game da kasuwar amfani Gona domin kaucewa lalacewar harkar Noman Baki daya a Najeriya.
Kamfanonin da suke harkar bayar da kayan Noma GA Manoma ayi Noma kowa ya amfana tsakanin Kamfanonin da kuma Manoma duk Lamarin na bukatar a duba Shi sosai.
Aminu Surajo Funtuwa ya bayyana hakan ne a lokacin wata tattaunawa da Manema labarai a ofishinsa da ke harabar Kasuwar a Funtuwa.
Aminu Surajo, ya ci gaba da cewa in dai Gwannati karkashin jagirancin Bola Ahmad Tinubu BA ta hanzarta yin abin da ya dace BA na ceton Manoma daga halin da suke cikin hakika lamarin Farashin Kayan Gona tare da Manoma na cikin wani mawuyacin halin da ke bukatar a duba lamarin sosai da idon basira.
“Ta yaya mutum manomi zai karbi Filin Gona ya sayi Takin zamani da tsada inda aka sayi Takin Yuriya Kan Kudi dubu 48 zuwa Sama da dubu Hamsin da biyu zuwa da Uku, sannan a sayar da Takin Kamfa Kan Kudi daga naira dubu Tamanin zuwa dari da biyu duk a wannan daminar da ta gabata, sannan kuma a samu irin wannan matsalar ta Farashin Kayan Noma BA daraja Sam. Ban da fa wannan akwai kudin Kayan Noma kamar feshin haki da na kwarai sai kuma kudin Tarakta tun kafin ayi shuka sai kuma kudin masu aikin da za su yi wa manomi aiki a gonarsa duk BA abin da ya sauka sai Karuwa ma kawai ya yi”.
Ya dace fa gwannati ta duba Babu wani Kayan da ke dawowa baya sai Kayan Gona duk abin da manomi ya sayar da kayan amfani da ya samu ma Gona idan ya ta fi sayo wani Kaya KO na aure KO gini duk babu sauki komai ya yi Sama.
” Kai masu sayen hatsin ma suna kokawa da matsalar Farashin nan domin kuwa Dan kasuwa na gudun Kada ya sayi Kayan a yanzu anjima kuma Farashin ya dawo kasa kaga asara Kada ta Shiga Ake hudu”.
“Wasu mutane ma da suke amsar Gonaki aro su yi Noma lallai hakika idan an bincika duk harkar ta Zama asara, akwai wani da ya ke shaida Mani cewa kudin Aron da ya bayar ma da ya lissafa sai ya GA lallai akwai ci baya, don haka a nan gaba idan ma Ka CE masa ya zo ga Gona Kyauta ma BA zai yi Noman na. Kuma Arewacin Najeriya Kashi Tamanin duk mun dogara ne ga Noma sai ya kasance Noman ya Zama na karamar asara Ake yi na, Manoma na sayar da kasa su a cikin sauki misali a lokacin da Ake sayar da Masara a Kan Kudi naira dubu Tamanin buhun Sinti naira dubu shida KO Bakwai yake, Amma a yanzu sai Ka saye Shi Kan dubu Tara zuwa har ma Goma, don haka a duba fa duk abin da Gwannati za ta yi ta na duba halin da Yan kasarta ke ciki, a duba bangaren Noma mutum nawa ya dogara da hakan kuma mutum nawa ne ke samun aikin yi da yawa a bangaren Noma.
Shin wai Tambaya a nan Shi ne mu BA zamu iya ciyar da Kan mu BA sai dai wata kasar ta ciyar da mu? Idan an duba bangaren Noma a yankin Funtuwa kawai za mu iya ciyar da jihohi Uku BA ma batun jihar Katsina BA, don haka gwannati ta duba kamar yadda ya duba koken talakawan ya dace kuma a duba harkar da Manoma za su samu ci gaba kowa ya samu saukin rayuwar Amma idan aka ta fi a haka BA Wanda zai Kara yin Noman KO ma sha’awa koda kuwa na ci ne sai mutum ya Gwammace ya saya a kasuwar BA ya Noma BA nan gaba.
Da Yake tofa albarkaci bakinsa Mataimakin shugaban Yan kasuwar Hatsi Alhaji Hamisu Jidadi, cewa ya yi hakika abin da ke Faruwa a game da kasuwar Hatsi lallai ci baya ne a yankin Arewa domin asara bayin Allah ke yi BA yar Kadan BA don haka idan Gwannati ba ta Farka ta duba wannan matsayin da muka Shiga BA akwai damuwa kwarai domin abin da zai biyo baya Allah dai ya kiyaye.
Na farko dai Ka amshi Gona da tsada manomi ya karbi Gona fadin hekta daya Kan Kudi naira dubu dari hudu kuma.idan Allah ya taimaki mutum ya Gyara ne mutum zai iya samun buhuna 40 KO Talatin da biyar, to, a kaddara ma Ka samu buhu arba’in kaga duk buhu ya kama dubu Goma Goma tun ma kafin a Gyara Shi sai aka zo a yanzu ana ta ya maka naira buhu naira dubu 25 zuwa dubu Talatin kaga kuma nawa aka biya Hari,huda da shuka sannan GA aikin Kaka GA kuma barazanar tsaro na wannan GA wancan daban daban duk GA Manoma suna fuskantarsu.
Saboda haka ne muke yin Kira ga Gwannatin da ta Kula fa kada a samu barazanar yunwa da Sauran wasu matsalolin saboda duk abin da za a CE za a sayo daga waje a kawo akwai fa lokacin da BA zai sawu BA.
“Kaga a baya Gwannatin da ta shude ta yi tsaro Mai kyau Kamfanoni suka Sanya aikin Shinkafa ana Gyara ta ana Yi Mata kilogiram Hamsin wannan Abu ne mai kyau Amma shigowar wannan Gwannatin lamarin na Neman duk ya shiriri CE don haka muke yin Kira ga Gwannatin lallai a ta fi da wancan taarin da Ake yi a can baya kowa ya samu ci gaba mu dogara da Kan mu Kada mu Zama lamarin ya sukurkuce mana ana sayo abinci daga waje indai fa BA a Noma abin da zai biyo baya to BA Shi da kyau Allah ya kiyaye, hakan CE ta Sanya muke yin Kira ga Gwannatocin Jihar da tarayya da su duba wannan lamarin fa da idon basira.
A bisa Binciken da wakilin mu ya yi a halin yanzu ya gano cewa kusan dukkan Kayan Kamfanonin da Ake sayer WA idan lokacin kakar Hatsi ta yi lamarin BA wani ci gaba Sakamakon rashin datajar da kayan amfani Gona suke yi Kayan Gini,Baburan hawa,gidaje,filayen,kwanon rufin gida da kusa da dai dukkan Sauran kayayyaki har ma da Bankunan da suke Hulda da masu sayowa Kamfanoni Kayan amfani Gona da kuma yin Huldar kasuwanci duk sun Shiga cikin wani halin da BA Wanda ya yi tsammanin faruwar hakan.
THESHIELD Garkuwa