Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnatin jihar Yobe ta tsaida ranar 25 ga watan Nuwamba 2023 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben kananan hukumomi.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Sakataren gwamnatin jihar (SSG), Baba Mallam Wali a wata wasikar sanarwa da ya aikewa hukumar zabe mai zaman kanta (SIEC) ta jihar Yobe.
Ya ce, “Na yi farin cikin isar da sakon amincewar mai girma Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni CON domin gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar 25 ga Nuwamba, 2023.”
A farkon makon nan ne dai Gwamna Buni ya rusa shugabannin kananan hukumomin jihar ne bayan karewar wa’adin su.
A wata mai kama da haka kuma majalisar dokokin Jihar Yobe ta sake tantance shugabannin riko na kananan hukumomin Jihar 17 da majalisar zartarwa ta mika musu.
Da ya ke bayyana batun amincewa ta ga manema labarai kakakin majalisar dokokin jihar Honarabul Ahmed Mirwa ya ce, sun yi hakan ne don cancantar su.
Kakakin majalisar ya kuma gargadi sababbin Shugabannin Rikon da cewar da zarar sun kama aiki su kasance masu mayar da hankali wajen gudanar da aikin su bi-hakki da gaskiya.
Cikin sababbin shugabannin kananan hukumomi 17 da ke Jihar da majalisar ta amince da su 14 daga cikin su tsofaffin shugabannin da suka sauka ne yayin da 3 daga cikin su na kananan Hukumomin Jakusko, Yunusari da Geidam duka sababbi ne.