Home / Labarai / Rukunin Farko Na Maniyyatan Nasarawa Sun Yi Hadari

Rukunin Farko Na Maniyyatan Nasarawa Sun Yi Hadari

Daga Imrana Abdullahi

Bayanan da muke samu na cewa rukunin farko na Maniyyatan Jihar Nasarawa da ke arewacin tarayyar Najeriya a kan hanyarsu ta zuwa filin Jirgin Saman Abuja sun samu hadarin Mota.

Su dai Maniyyatan masu aniyar tafiya kasa mai tsarki domin yin aikin Hajji sun fito ne daga Jihar Nasarawa da ke Arewa ta tsakiyar Najeriya Suna kuma kan hanyarsu ne ta zuwa babban filin Jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Aziekuwe da ke Abuja, sai suka hadu da hadari a kan hanya.

Wata majiya daga hukumar Alhazai ta Jihar ta ce hadarin dai ya faru ne a ranar Laraba, a wani wurin da ake kira “kara” da ke da wata kasuwar Dabbobi a karamar hukumar Keffi a cikin Jihar Nasarawa lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Abuja,

da nufin a ranar Alhamis 25, ga watan Mayu, 2023. su ta fi kasar Saudiyya,domin sauke farali.

Sai dai majiyar ta tabbatar mana da cewa babu wanda ya rasa ransa kuma wadanda suka samu raunuka suna wani asibiti a cikin Jihar ana duba lafiyarsu.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.