Home / News / Abdu Maikaba Na Neman Kulab Din Da Zai Dauke Shi

Abdu Maikaba Na Neman Kulab Din Da Zai Dauke Shi

Abdu Maikaba Na Neman Kulab Din Da Zai Dauke Shi

Mustapha Imrana Abdullahi
Sanannen mai horar da kungiyoyin wasan kwallon kafa a tarayyar Najeriya Abdu Maikaba ya bayyana cewa a shirye yake ya amsa tayin da duk wani kulab din wasan kwallon kafa zai yi masa domin ba su horo.
Maikaba ya shaidawa jaridar wasanni ta SPORTINGLIFE cewa tuni ya kammala aikin kwantaragin horar da kungiyar wasan kwallon kafa ta Filato na shekarar 2020 zuwa 2021, bayan kammala aikinsa na shekaru uku da kulab din.
Maikaba ya dai ce ya na matukar jindadi kwarai da irin aikin da ya yi na shekaru uku inda ya yi godiya ga kulab din da damar da ya samu na horar da yan wasan tsawon shekaru uku.
“Na kammala aikin horar da yan wasan kulab din na tsawon shekaru uku, don haka a yanzu ina neman kulab din da zai dauke ni wani aikin ne,” inji Maikaba.
Maikaba dai ya samu nasarar yin aiki da wasu kulab din Wikki Touris,mulan din Enyimba ta Aba, kungiyar kwallon kafa ta Akwa,kungiyar kwall9n kafa ta Abuja.
Abdu Maikaba ya kuma samu nasarar samun lambobin yabo a shekarar 2017 ta Aitero lokacin ya na horar da kungiyar kwallon kafa ta Akwa
Ya kuma yi aiki a matsayin mataimakin mai horar da yan wasa karkashin mai horar da wasa Paul Aigbogun lokacin wasanni yan kasa da shekaru 20 a shekarar 2019 lokacin wasan yan kasa da shekaru 20 na Afrika (AFCON) da kuma yan kasa da shekaru 20 na hukumar wasan kwallon kafa ta duniya FIFA.

About andiya

Check Also

KADCCIMA ON  ON REVIEW OF ELECTRICITY TARIFF

    Following approval by the Electricity Regulatory Commission (NERC) for the increase of electricity …

Leave a Reply

Your email address will not be published.