Home / Labarai / ABDUL’AZIZ YARI ZAI BUDE OFISOSHI 6 A MAZABARSA

ABDUL’AZIZ YARI ZAI BUDE OFISOSHI 6 A MAZABARSA

Ofishi Shidda (6) Ne Za A Bude Domin Samun Damar Kara Kusantar Jama’a Da Wanda Suka Zaba A Matsayin Sanatan Yankin Zamfara Ta Yamma, Za Dai A Bude Ofisoshi Ne A Kananan Hukumomin Talatar Mafara, Bakura, Maradun, Anka, Bukkuyum Da Karamar Hukumar Gumi.
Sabon Zababben Sanatan Yankin Zamfara Ta Yamma, Tsohon Gwamna Andul’Aziz Abubakar Yari Ne Ya Yi Wannan Alkawarin A Lokacin Da Yake Jawabi Ga Dimbin Jama’ar Da Suka Kai Masa Ziyarar Bangirma Da Kuma Taya Murnar Lashe Zaben Da Ya Yi.
Mutanen Bakura Dai Sun Je Gidan Zababben Sanatan Ne Da Ke Garin Talatar Mafara Karkashin Karkashin Kungiyar Bakura Development Forum Inda Suka Taya Shi Murnar Cin Zaben.

Sai Sanata Yari ya godewa mambobin kungiyar bisa ziyarar da suka kawo masa ya kuma yi godiya kwarai ga mutanen karamar hukumar Bakura bisa irin gudunmawar da suke bayarwa, abin da ya ce shi ya yi sanadiyyar samun nasararsa a zaben da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata.

Yari ya ci gaba da bayanin cewa ya na da wani ingantaccen tsarin dabzai yi amfani da shi domin jin dadin mutanen mazabarsa, sai dai ya yi kira da a ci gaba da samun hadin kai domin a samu nasarar ci gaban da kowa ke bukata.

“Zan yi shawara da masu ruwa da tsaki a wannan yankin dan majalisar da nufin samun mutanen da suka cancanta za su iya yin aiki a ofisoshin da za a bude na shiyyar a kananan hukumomi shidda (6).

Ya ce zai kuma yi kokari wajen samawa mutane ayyukan yi a matakin Gwannatin tarayya.

Tun da farko da yake jawabin Gabatarwa shugaban kungiyar al’ummar Bakura, Alhaji Mustapha Rabi’u Bakura,cewa ya yi wannan ziyarar na da matukar amfani kwarai domin taya murna ga sabon zababben Sanatan shiyyar Yammacin Jihar Zamfara.

Mustapha ya kara da cewa shiyyar da kuma Jihar Zamfara baki daya ba za su ta ba mancewa da irin ayyukan raya kasa da zababben Sanatan Sanatan aiwatar ba a lokacin Mulkinsa na Gwamna.

Kamar yadda Mustapha ya bayyana cewa a tsawon shekaru Takwas na mulkin Abdul’Aziz Yari an samu ci gaba a bangaren samar da ruwan sha, samar da hasken lantarki, gina tituna, ciyar da ilimi da harkokin lafiya gaba ayyukan da ba za a mance da su ba a tsawon shekaru Hamsin nan gaba masu zuwa.

Sai Mustapha ya bayar da shawara ga zababben Sanatan da ya ci gaba da zamowa mai yi wa jama’a hidima tare da yi masu kyakkyawan wakilci a majalisar Dattawa ta kasa ya kuma yi addu’ar Allah ya bashi shugaban majalisar Dattawa ta kasa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.