Home / Kasuwanci / SANA’AR WALDA TA YI MANI KOMAI – Muhammadu Kabiru

SANA’AR WALDA TA YI MANI KOMAI – Muhammadu Kabiru

Daga Imrana Abdullahi

MUHAMMADU KABIRU MUSA SADO wani mai sana’ar Walda ne a garin Talatar Mafara a Jihar Zamfara arewacin tarayyar Najeriya da ya shaidawa wakilin mu cewa sana’ar ta yi masa komai.

Muhammadu Kabiru Musa Sado ya ce sana’ar Walda ta yi masa komai kuma ya Gaji sana’ar ne ga mahaifinsa domin ba wani wuri ya ta fi koyon ta ba, amma na ta fi kwalejin kimiyya da fasaha ta Gwamnatin tarayya da ke Kaduna sai kuma ya koma Birnin Kebbi nan ma ya kasa ci gaba da yin karatun.

Amma cikin ikon Allah tun da ya na da basira irin wannan sai kawai mahaifi na ya rike ni na ci gaba da sana’ar Walda a haka nan.

Muhammadu Kabiru ya ci gaba da cewa cikin irin ayyukan da yake yi akwai Kofofi na karfe da kuma na Alminu’om da sauran kafofin da kamfanonin zamani ke yi, kai wadansu kofofin ma a nan duk a wuri na aka fara ganinsu domin ni idan naje wurare irinsu Kaduna sai in rika duba kofofi masu kwalliya iri iri idan na zo gida sai in yi su kuma mutane su Karbe su a rika ba mu aikin yin su.

Akwai kuma aikin hada Fila – fila mutane na saye suna aikin ginin Gidaje da kuma aikin sarrafa karafuna daban daban domin amfanin jama’a da dai sauran abubuwa na sana’a Gwargwado muna iya yinsu.

A game da batun kera Jirgin Sama da aka yi kuwa a garin Talatar Mafara, Sai Muhammad Kabiru ya ce to a kan wannan hakika mahaifina ne ke karfafa mana Gwiwar cewa a kullum ayi wani abu da zai karfafa mana Gwiwar ayi wani abu da ke dauke da fasahar kirkire- kirkire mutum ya sarrafa ya kuma aiwatar da shi. A gaskiya shi mahaifina ne keda akalla kashi Tamanin na wannan Jirgin na sai an yi shi.

“Saboda ni matata ta biyu, yar Kaduna ce don haka ne idan naje sai in rika duba wa in dan dauko wani launin aikin, musamman irin Kofofin da za a Sanya masu kwalliya kamar zaiba ko Gwal da dai sauransu, a gaskiya ba alfahari ba ni na fara zuwa da wadannan abubuwan nan Mafara tun da ka san yawo ilimi ne don haka idan ka taho sai ka hada nan da can ya bada wata ma’ana har mutane suyi amfani da shi kuma idan ka hada sai kaga naka ma ya fi nasu domin kai ka ta fi wurare uku a kalla.

A game da yin wannan Jirgin sama Muhammad Kabiru ya ce an samu hukumomi da yawa sosai “ko can inda kuka je shi wancan kanina ne kunga an karu kwarai ya koma wani wuri shima ya kama nasa aikin”.

Ya ce shi duk da irin halin da aka shiga na tsadar kayan masarufi amma bai rage ma’aikata ba ana nan tare ana yin aikin. Kuma ni a gaskiya yara na suna da hakuri saboda duk ranar da babu sai suyi hakuri, domin a cikinsu akwai kanne na masu iyali akwai kuma wadanda ba kanne na ba masu iyali da wadanda ba su da iyali duk muna tare a wannan aikin sana’ar Walda

Yan yaran ma su na fi ba kudi musamman ma a wannan lokacin da ake da tsarin asusun ajiyar kudi. Mutanen da na yaye a nan sun kai Ashirin, kuma a yanzu ina tare da mutane sun kai Goma sha Takwas (18) wajen aikin aluminium da wajen masu fenti da ainihin masu aikin Walda.

Muhammadu Kabiru ya kuma yi kira ga matasa da su tashi tsaye wajen koyon sana’o’in da za su tallafa masu.

Misali ” ni da na kammala makarantar Sakandare a shekarar 1990 kuma mahaifina mai hali ne mun dan saba da wahalar amma kadan da abubuwa suka canza sai mahaifina ya ce sai na yi aikin sai kawai Naga an matsa Mani sosai lokacin ina yaro har sai na ce ni Allah yasa in makance wannan wahala ta ishe ni. Saboda haka sai na yi hijira daga nan zuwa garin Gusau a kan bani son aikin amma da Kakana ya gane ni ya ce me yakawo ka yaga abin da na saba idan na yi kwana daya biyu sai in koma amma sai ya ga na kusa sati guda sai ya tambaye ni na ce masa baba na ne ke ban wahala kaji – kaji sai ya yi ta Sanya ni aiki ya na wahal dani ni kuma ban saba da wahala ba.

Sai kawai ya yi Mani dabara ace haba Jika na na farko za a cewa ya wahala? Bar ni da shi lokacin ina yaro na kammala makaranta zan iya karatu da rubutu. Sai ya bani wata  Takarda ace Mani idan kaje ka bashi ita kawai inga yadda zai sake saka aiki ya bani kudin mota sai ya sayo Mani sababbin kaya masu kyau na Sanya na taho, amma koda na samu wani abokina sai ya ce shin wai kai daga an baka takardar sai ka amso baka san kome ta kunsa ba. Nan take ya bani shawara mu bude takardar nan muna budewa sai Naga ya rubuta cewa aikin da ake Sanya ni a nunka shi sosai kuma a bani sai na yi shi, kaji dabara irin ta manya.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.