Home / Ilimi / Adamu Atta Ya Dauki Nauyin Yara Dubu 12 Su Yi Karatu

Adamu Atta Ya Dauki Nauyin Yara Dubu 12 Su Yi Karatu

 

Mustapha Imrana Abdullahi

 

 

A kokarin ganin ya ci gaba da Tallafawa al’ummar Jihar Kaduna,Najeriya da nahiyar Afrika baki daya mai kishin jama’a domin ganin kowa ya tsaya da kafafunsa Alhaji Adamu Atta ya dauki nauyin yara a kalla dubu Goma sha biyu da ga garin marabar Jo’s cikin Jihar Kaduna domin yin karatu kyauta.

 

 

Alhaji Adamu Atta wanda shi ne mai kulab din kwallon Dawaki ta (Fift Cochar) da ke garin Marabar Jos ya sanar da hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai lokacin bikin ranar yara ta duniya da aka yi a makarantar Firamare da ke filin wasan kwallon Dawaki a marabar Jos da ke karamar hukumar Igabi cikin Jihar Kaduna.

 

 

Kamar yadda Adamu Atta ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya aiwatar da wannan aikin daukar nauyin yara dubu sha biyu su samu damar yin karatu shi ne domin bayar da hakkin jama’ar da yake amfana da su na su hakkin.

 

 

“Abin da ya sa shi ne idan muna son kasar nan ta ci gaba dole sai an hada Gwiwa baki daya a tabbatar cewa kowa da ke cikin wannan kasar sai an ba yayansa damar yaransa su ta fi makaranta shi kuma ya samu abin yi, in ana son a zauna lafiya cikin kasar nan saboda haka a cikin wannan makarantar za a samu dalibai Sama da dubu Goma sha biyu”. Inji shi.

 

 

Hazalika Adamu Atta ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da yin hadin Gwiwa da Gwamnatin Jihar Kaduna da kuma kungiyoyi bayar da agaji da kuma masu hannu da shuni domin bunkasawa tare da samar da ingantaccen ilimi musamman na yayan marasa galihu.

 

Ya ci gaba da cewa “kowa ya kawo ta sa gudunmawar ba a rungume hannu a zauna ana jiran sai Gwamnati kawai, wannan ba dabara ba ce saboda Gwamnati komai akwai iyakarsa mu kuma muna ganin cewa wadanda suke da hali, ko kuma suke da hanyar nemo masu halin idan aka hada Gwiwa za a cimma nasarar wannan abubuwan da ake da su, idan aka samu yara suka samu makaranta suka ko yi sana’a rigingimu da muke samu tare da rashin samun ayyuka hakika ai za a ga saukinsu domin ci gaba zai maye gurbinsu don haka muna neman gudunmawar kowa cewa mu hada kai mu kawo shawarwari a kuma kawo gudunmawar da za a dai- daita wannan harkar.

 

Ana tsokacin kwamishinan ilimi na Jihar kaduna Malam Shehu Muhammad cewa ya yi hakika abin da Adamu Atta ya aikata abin a yaba ne domin Namijin kikari ne kwarai saboda kowa ya ga irin yadda ya tsara lamarin zai kawo tsarin karantawa da na’ura mai kwakwalwa.

 

 

Saboda haka “muna tabbatar masa da jama’ar martabar Jos Gwamnatin Jihar Kaduna ta hanyar ma’aikatar ilimi za ta bashi dukkan gudunmawar da yake bukata za a taimaka wa yaran nan su cimma burinsu fatar mu kawai shi ne wadannan yara su zamanto hazikai kuma zakakurai a kasa baki daya kuma za mu Sanya wannan wuri ya zama inda za ta zama cibiyar da za a rika koyo a hannunsu ta bangaren ilimi, don haka muna godiya ga abin da aka yi Allah ya saka masa da alkairi”.

 

 

Kwamishinan ya kuma dauki alkawarin kara horar da malamai da kuma kara gina ajujuwa a makarantar.

 

Sarkin Marabar Jos Alhaji Adamu Sa’idu da Sarkin Kudin Marabar Jos Malam Adamu Sidi duk godiya suka yi ga Adamu Atta da ya ba yayansu damar samun ingantaccen ilimi kyauta.

 

 

“Hakika mu na godiya ga Allah da ya fitar mana da wannan ni’ima yadda wannan bawan Allah ya auki nauyin samar wa yayan mu ingantaccen ilimi kyauta, Wannan lamari ci gaba ne a gare mu sai godiya ga Allah da shi Adamu Atta.

 

 

Muna godiya kwarai Allah ya yi albarka ya kuma amfana abin da aka yi da wanda aka bari Allah ya daukaka wannan makaranta mun gode mun gode.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.