Home / Labarai / Allah Ya Yi Wa Isma’ila Isa Funtuwa Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Isma’ila Isa Funtuwa Rasuwa

Imrana Abdullahi

Sanannen shahararren dan kasuwa kuma masanin harkokin wallafa Jarida daya daga cikin shugabannin harkar yada labarai, Malqm Isma’ila Isa Funtuwa ya rasu.

Ya dai rasu ne a garin Abuja a lokacin da ake duba lafiyarsa. Ya rasu yana da shekaru 78 a duniya.

Bayanai dai sun bayyana cewa ya yi fama da ciwon zuciya a lokacin da ana duba lafiyarsa.

Masanin harkokin mulki da ya kasance shi a gida da kasashen waje kuma masanin harkar masaku, rahotanni sun bayyana cewa a lokacin da jikinsa ya yi tsami shi ya tuka matarsa da kansa zuwa asibiti domin neman magani.

About andiya

Check Also

An Zargi PDP Da Ayyukan Ta’addanci A Jihar Zamfara

Gamayyar Kungiyoyin Kwararru Na Dattawan Arewa Sun Kalubalanci Kalaman PDP A Game Da Batun Tsaron …

Leave a Reply

Your email address will not be published.