Bashir Rabe Mani
Idan dai zaku iya tunawa a ranar Litinin ne 20 ga watan Janairu 2020 kotun kolin Nijeriya tayi Watsi da batun daukaka karar da Alhaji Ahmed Aliyu da kuma Jam’iyyarsa ta APC suka yi bisa dalilin da kotun ta bayyana da cewa babu wata hujja. Inda ta bi irin hukuncin da kotun da ke kasa da ita ta yanke.
Kamar yadda mai Shari’ar kotun daukaka kara ta Sakkwato mai shari’a Uwani Abba Aji, ta yanke hukuncin cewa ta kori karar da mai kara Ahmed Aliyu na jam’iyyar APC APC shigar yana karar zaben Tambuwal Tambuwal sabawa tanaje tanajen tsarin gudanar da zabe da kuma tsare tsaren hukumar Zabe domin gudanar da zaben kansa don haka kotun farko da ke sauraren kararrakin Zabe ta yi kuskure a kan king yin amfani da hujjojin da aka gabatar gabanta na yin zabe sama da yawan mutanen da yakamata su kada kuri’a da kuma wadansu hujjojin da aka gabatar mata na karya dokokin zabe a lokacin zaben 9 da 23 ga watan Maris 2019.
Mai shari’a ABBA Aji ta ce Ahmed Aliyu da APC sun kasa alakanta hujjojinsu da tushen karar da suka yi ta kara da cewa don haka ba kotu ce za ta kama binciken tabbatar da hakan ba.
Don haka ne batun maganar karar da aka daukaka zuwa kotun daukaka kara da dan takarar Gwamna na APC da Jam’iyyarsa suka shigar a kan zaben Gwamna da kuma ragowar zaben sun bar wadansu tambayoyin da har yanzu ba a amsa su ba domin tambayoyin sun fi amsoshin yawa kwarai matuka. Domin aikin karkacewar shari’ar sun saka masu kaunar tsarin Dimokuradiyya cikin rudu da tunanin yadda al’amuran za su kasance.
Mutanen Nijeriya da dama sun yi ta mamakin yadda lamarin hukuncin ya kasance daga kotun kolin kasar, wanda hakan ya sanya wa jama’a da dama sake tunani a kan kotun da al’amuranta. “Inda masana harkar shari’a da dama suka rika yin bayanin cewa batun hukuncin ya tsaya a yin hukuncin ne amma ba adalci ba”
Kamar yadda zantuttukan magabata Duke cewa ” Idan abin da ka aikata ya sanya saura da dama yin tunani ko mataki sosai,sula yi koyi da abin kwarai, sula kuma aikata shi sosai, lallai babu shakka kai shugaba ne”.
“Kirkire kirkire suna bambanta mutane tsakanin shugaba da mabiya. Kada la bi inda hanya za ta kai. Ka ta Fi kawai wurin inda ba hanya ka bar tarihi”. Saboda haka babban jagoran mu mai taimako da Kishin jama’a jagora abin koyi Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, hakika shugaba ne na kwarai. Wannan babu mai iya kankare hakan domin shi ne gaskiya hakan yasa dimbin jama’a da dama suke yi masa mubaya’a da bashi cikakken goyon baya had bayan ma da aka kammala yanke hukuncin kotun koli da ke Abuja.
Hakika duk wanda ya nuna goyon baya da mika cikakken hadin kai ga mutum mutane na kowa da kowa, Ahmed Aliyu da APC suna farin cikin bayyana goyon bayansu tare da amincewa da Sanata Wamakko. Domin sun bayyana wa duniya cewa har yanzu, gobe da Jibi shi ne shugabansu, duk inda ya nufa kuma duk abin da yake yi lallai suna tare da shi. Hakika irin wannan lamari yana faranta zuciya yasa ta yi fari sosai tare da dimbin annashuwa. Mutane da yawa a ranar Larabar da ta gabata 22, 2020, sun muna hakan sun kuma yi nasarar muna wannan goyon baya ga Sanata Wamakko, Ahmed Aliyu, APC da kuma wadanda suka kasance suna bayan irin nasarar da APC ta samu.
Duk da irin yanayin sanyin da ake ciki amma sai da jama’a suka fito da yawa domin muna goyon baya ga jam’iyyar APC tare da manyan jagororinta irin su Wamakko da Aliyu inda suka cika garin Sakkwato baki daya suka tarbi jagoran jam’iyyar a Jihar Sakkwato Sakkwato arewa masu Yamma kasar baki daya Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko tare da mutanen da yake tare da su daga Abuja.
Sauran wadanda yake tare da su sun hada da shugaban kwamitin tsaro na majalisar Dattawa, Ministan ma’aikatar kula da harkokin yan sanda, kuma shugaban babban kwamitin zaben Gwamnan jihar Alhaji Muhammadu Maigari , tsohon ministan harkokin sufuri kuma Darakta Janar na kwamitin zaben Gwamnan Jihar dan takarar Gwamna na APC Alhaji Ahmed Aliyu Sakkwato, da mataimakinsa Alhaji Faruku Malami Yabo da shugaban Jam’iyyar APC Alhaji Isa Sadiq Achida, da sauran dubban Mugabe suna ta murna tare da farin ciki,cikin annashuwa.
Da yake wa dimbin nagoya bayan jawabi, Sanata Wamakko shawartar yayan jam’iyyar ya yi tare da dukkan mutanen jihar Sakkwato da su suna lafiya su ci gaba da hada kansu da yin addu’a ya kuma yi godiya fa Allah madaukakin Sarki da irin yadda jama’ suke bashi hadin kai da goyon baya tare APC.
Ya kara da cewa a matsayinmu na musulmi mun yarda da Allah kuma.mun karbi abin da ya shame my da kyakkyawar manufa, “Ya kuma lokaci ainihin al’Umar jihar Jihar su fito a ranar larabar su zabe dan takarar APC a zaben da za a yi.
Da yake gabatar da nasa jawabin ministan kula da harkokin yan sanda, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi, cewa ya yi hakika yana godiya ga Allah ganin irin yadda yayan jam’iyyar APC suna nan dunkule a wuri daya duk da abin da ya faru na batun kotun daukaka kara. Yayan APC suna nan kamar yadda aka sansu da karfinsu suna ka cike da kwarin Gwiwar samun nasara, ” A matsayin mu na musulmi abin da ya faru lamari ne daga Allah don haka mun karbeshi da aniya mai kyau”, inji ministan.
A nasa jawabin dan takarar jam’iyyar APC, Alhaji Ahmed Aliyu Sakkwato, bayuana abin da aka yi wa jam’iyyar ya yi a matakin kotun sauraren kararakin Zabe da kotun daukaka kara da kuma kotun koli da cewa fashi da makami ne da rana tsaka, Aliyu ya ce irin goyon bayan da jama’a suka ba APC an kwace shi ta hanyar sabawa doka don haka ya bayar da tabbacin cewa Allah zai yi sakayya.
Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Sakkwato, Alahji Isa Sadiq Achida, tabbaci ya bayar da cewa sama da kashi 70 na al’ummar Jihar Sakkwato suna bayan APC.Kuma ba za su koma PDP ba kamar yadda Gwamnan Jihar tare da na kusa da shi suka nema.
Masha Allahu, dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah da ya azurta al’ummar Jihar sakkwato da mutumin da bai gajiyawa wajen taimakon al’umma tsohon maganin da ya dade ana damawa da shi a harkokin duniya da ya zama Gwamna karo biyu, tsohon mataimakin Gwamna kuma Sanata mai ci a halin yanzu da ke gudanar da aikinsa kai tsaye a majalisar kasa domin ciyar da kasar gaba hakika akwai ban sha’awa iron yadda jama’ar jihar Sakkwato bakai daya suke tare da shi suna bashi goyon baya hakazalika dansa Ahmed Aliyu tare da APC godiya mara adadi.
Mani, mataimaki na musamman ne a kan harkokin kafafen yada labarai da fayyace bayanai ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya kuma yi wannan rubutun ne daga Sakkwato.