Home / Labarai / Aminu Sani Jaji Ya Raba Tirelolin Abinci 35 Ga Mabukata A Jihar Zamfara

Aminu Sani Jaji Ya Raba Tirelolin Abinci 35 Ga Mabukata A Jihar Zamfara

…Ya shawarci Jama’a su ci gaba da addu’o’in neman taimakon Allah
Dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kauran Namoda da Birnin Magaji Honarabul Aminu Sani Jaji, ya kaddamar da fara rabon kayan abinci ga al’ummar Jihar Zamfara musamman ma mabukata.
Honarabul Aminu Sani Jaji ya kaddamar da rabon kayan abinci da suka kai yawan Tireloli 35 ga jama’a fisabilillah, a wannan watan Azumin Ramadana mai albarka.
Kamar dai yadda taron ya gudana a garin Gusau babban birnin Jihar Zamfara, Honarabul Jaji ya sanar da hakan ne a ranar Talatar da ta gabata lokacin kaddamarwar da dimbin al’umma suka halarta.
Dan majalisar ya yi kira ga daukacin al’umma da su yi amfani da wannan watan na Ramadana wajen yin addu’o’in samun taimakon Allah domin kawo karshen matsalar tsaron da ke yi wa jiha da kasa kalubale.
Kamar yadda dan majalisar ya bayyana cewa lamarin matsalar tsaro ya shafi dukkan kowa don haka yake bukatar sai kowa ya Sanya hannu domin kawo gudunmawar a kawar da shi.
” Ya dace mu taimakawa Gwamnati a kowane irin mataki domin su samu nasarar samar da tsaro da zaman lafiya a tsakanin al’umma
“Wannan watan na Ramadana wata ne na neman tsira da gafarar ubangiji Allah don haka mu kara matsa kaimin yin addu’o’in samun taimakon Allah domin kawo karshen matsalar tsaro”, inji Jaji.
SSI Honarabul Jaji ya yi kira ga jama’ar Jihar Jihar su guji mayar da batun tsaro lamari na siyasa ko kuma yin siyasa da bangaren tsaro a Jihar.
Ya kuma yi kira a kan bukatar da ake da ita na samun hadin kai tsakanin masu ruwa da tsaki a Jihar domin samun damar magance matsalar tsaron da ke zamarwa Jihar Kalubale
Da yake gabatar da jawabi shugaban Dattawan jam’iyyar APC na Jihar Zamfara, Alhaji Lawal Makaman Kaura ya bayyanaabin da  dan majalisar ya yi da cewa abin a yaba tare da yin murna ne domin ci gaban jama’a.
Makaman Kaura ya ci gaba da cewa hakika wannan saukin da dan majalisa ya kawo zai taimakawa dimbin al’umma su samu sauki musamman a tsakanin mabukata.
Tun da farko shugaban kwamitin rabon kayan abincin, Alhaji Abubakar Aliyi cewa ya yi dan majalisar ya kawo dauki ga jama’a da kayan abinci da suka kai Tireloli 35 da sula hada da buhuna Shinkafa, Gero, Suga da Hatsi.
Aliyu ya kara da cewa wadanda za su amfana sun hada da marayu, mutane masu bukata ta musamman, kungiyoyin Mata da matasa, shugabannin APC da suke a dukkan mazabu 147 daga kananan hukumomi 14 na Jihar.
“Sauran sun hada da shugabannin jam’iyya na jiha da kananan hukumomi, an kuma Dorawa shugabannin jam’iyya na mazabu alhakin rabon kayan a cikin jiha”, inji shugaban kwamitin rabon.
An dai samu wadansu mutane daga Jihohi da dama da suka kasance suna cikin garin Gusau da suka halarci babban taron rabon kayan.
Sai dai kaji al’umma na cewa Honarabul Aminu Sani Jaji ne ya taho, muna yin godiya kwarai.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.