Duba da irin yadda Sanata Aminu Waziri Tambuwal ke kokarin ganin harkokin al’ummar Jihar Sakkwato da Najeriya baki daya sun bunkasa ya sa aka kira wani babban taron masu ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP da suka fito daga daukacin kananan hukumomin Jihar baki daya inda aka tattauna muhimman batutuwan ci gaba da za su amfani kowa.
Sakamakon irin yadda wannan taron ya gudana tare da masu ruwa da tsakin jam’iyyar PDP, kamar yadda aka bayyana irin yadda ake gudanar da harkokin mulki a Najeriya a matsayin lamarin da bashi da bambanci da mulkin soja amma ba Dimokuradiyya ba kasancewar Dimokuradiyya tsari ne da ke tabbatar da yanci da kuma martabar kowa a cikin kasa ba tare da la’akari da wani bambancin addini akida ko al’ada ba.
Shugaban matasa na jam’iyyar PDP a yankin Arewa maso Yamma Alhaji Atiku Muhammad Yabo Sarkin Yakin Yabo”ne ya bayyana hakan a cikin wata tattaunawa da ya yi a faifan bidiyo.
Atiku Yabo ya ci gaba da bayanin cewa irin yadda al’amura ke gudana a Najeriya da sunan Dimokuradiyya hakika lamarin ba Dimokuradiyya ba ne wani al’amari ne kawai mai kama da mulkin Soja da ake tafiya da yan uwa da abokan arziki kawai.
Idan ba yan uwa da abokai ba babu wani mutum da ake saurara ma wa a yadda ake tafiyar da mulkin Najeriya a halin yanzu”, inji Atiku Yabo
“Amma dai Talakawa ko yan siyasa duk wannan ba wa’a ma sanin ko yana nan a raye domin ta harkar su kawai suke yi”
Sarkin Yakin yabo ya ci gaba da bayanin cewa a wani taron da aka shirya na masu ruwa da tsaki a Jihar Sakkwato karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Sakkwato, tsohon kakakin majalisar wakilai na tarayya kuma tsohon shugaban dandalin Gwamnoni sannan tsohon shugaban kungiyar Gwamnonin PDP wanda a halin yanzu shi ne Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Kudu Alhaji Aminu Waziri Tambuwal.
“Hakika duk wanda ke cikin jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato ya na tare da shugabancin sa saboda a lokacin da ya yi Gwamna al’ummar Jihar Sakkwato duk sun amfana kwarai ya yi kokarin canza tarbiyyar matasa sannan ya kawo abubuwa na ci gaba domin gyara kowa ya Sani ba wai sai an rubuta a midiya ba don haka duk wanda ke Jihar Sakkwato ya san Sanata Amini Waziri Tambuwal shugaba ne da za a bi shi sau da kafa, hakan ne yasa aka tara jama’ar da suke birni da kauye a Jihar Sakkwato domin tattaunawa yadda jam’iyyar za ta Farfado”.
Ita dai PDP ga duk wanda ya Santa hakika ya san cewa jam’iyya ce ta hadin kan kasa ba ta yanki ba domin al’umma su amfa a cikin kasar su a koda yaushe domin jama’a shaida ne a shekarun da ta yi mulki an ga irin amfanin da aka samu na karuwar tattalin arzikin kasa, an taimakawa Noma, lafiya da shugabanci duk wannan kowa ya shaida hakan ba bangaranci ba wani bambanci a tsarin har kuma a yanzu al’ummar Najeriya na tuna hakan suna cikin shauki da began PDP
A game da irin gwagwarmayar Sanata Aminu Waziri Tambuwal kuwa sai Atiku Yabo ya ci gaba da bayanin cewa duk wanda ya san Sanata Aminu Tambuwal ya san irin gwagwarmayar da yake yi ta ganin kasa ta ci gaba da haduwa wuri daya al’umma su samu ci gaba.
” Ko a halin yanzu kowa ya Sani cewa yan farfaganda da suke ta yaudarar al’umma da cewa ana yin kasa da kasa misalin an lalata tattalin arzikin kasa duk dai wasu hanyoyin yaudara sai da aka tabbatar da su aka kuma yi amfani da su. Amma shi Allah baya zalunci kuma baya bari ayi zaluncin domin a yanzu jama’a sun gane sun fahimci komai musamman a irin yadda tattalin arziki da tsaro ke ciki, a halin yanzu duk wani da ke cikin kasar nan birni da kauye ya san meye ke bambancin Gwamnatin PDP da na wata jam’iyya mai mulki a Sakkwato wata APC”.
” Kokarin da Sanata Aminu Tambuwal ya yi tun a lokacin da yake Gwamna hakika ya taimaka domin matasa da dama sun samu sautin cewa sune da za su Arizona dama da su ko a nan gaba. Kuma mu kan mu irin wannan kokarin ne ya Sanya muka ga ya dace mu shigo a dama da mu a harkar ta yadda za a samu nasarar sauya wadansu abubuwa kowa ya ci gaba”.
“Kamar yadda kow Aya Sani a lokacin da jam’iyyar PDP na mulkin Jihar Sakkwato karkashin jagorancin Aminu waziri Tambuwal da Najeriya kowa ya Sani mata iyayen mu mata ba su fita suna tserewa domin yunwa ko kishin ruwa. Amma da zarar an ce jam’iyyar APC kowa ya san ita ta Sanya jama’a su gudu su bar iyalansu a cikin gida ba ci ba sha don haka abin da ake yi a halin yanzu mulki ne ba jagoranci ba kuma shi duk wanda ya Sani taarin dimokuradiyya tsari ne na jama’a su samu walwala da jin dadi a koda yaushe, ana yi ne kawai kamar yadda ake so harkar ta koma ta yan uwa da abokan arziki kawai su kadai ake saurarawa amma shi talaka ko dan siyasa ba ka iya fitowa ka ce ga abin da yake aikatawa a cikin kasa Kona Gwamnatin kasar sa ko domin ganin wai da shi aka kafa gwamnati, idan ka duba a can baya lokacin shugaba Obasanjo ya yo shari’a da mataimakinsa kusan shari’a Goma sha biyu kuma shugaban kasar bai yi amfani da wani abu ba ko don ya nuna karfin Mulkinsa ya samu nasara amma dai a lokacin dan Najeriya ba sai an tambaye shi ba wace jam’iyya ce ke mutunta dan Najeriya ta mutunta shugabanci don haka kowa ne dan Najeriya ya san abin da aka yi ya saba da abin da ke faruwa a halin yanzu.
Alhamdulillahi abin da nake bukata a nan shi ne in jawo hankalin matasa a Jihar Sakkwato su Sani cewa kar su sake su mance da irin mutunta wa da karramawar da ake yi masu a Jihar Sakkwato da kasa baki daya musamman irin yadda ake mutunta su a karramasu a koda yaushe domin jam’iyyar PDP ta kowa ce da keda izinin shigar ta a koda yaushe saboda ba ta wani ko wasu bace kuma a saurare shi ya bayar da tasa gudunmawar kuma a saurare shi domin a samu ci gaba
Saboda haka kira na ga yayan jam’iyya a nan shi ne zaben shugabannin Mazabu ya kusa zuwa da jama’ar PDP su Sani shugabanci kamar Kalihu be Allah ke bayarwa ba wai domin kashin kansa ba ne ya ba kansa kuma Allah ne ke bayarwa son haka kamar kalihu ne ba don kashin kansa ya ba kansa ba