Fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ta sanar da ganin watan Azumin Ramadana na wannan shekarar.
Sanarwar ta fito ne daga Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Janaidu, inda sanarwar ta ce an ga watan a sassa daban daban a wadansu wurare a Najeriya.
Saboda haka da wannan sanarwar gobe Laraba ne daya da watan Azumi kenan.
Fata dai Allah ya bamu ikon yin azumin cikin koshin lafiya da walwala kuma Allah ya karbi Ibadun mu
THESHIELD Garkuwa