Home / Ilimi / An Gano Haramtattun Jami’o’i 49 A Najeriya

An Gano Haramtattun Jami’o’i 49 A Najeriya

….AN GANO HARAMTATTUN JAMI’O’I A NAJERIYA

A kokarin Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban Muhammadu Buhari na ganin an gyara harkokin ilimi domin a samu ilimi mai inganci ya sa hukumar da ke kula da jami’o’I ta kasa (NUC) karkashin jagorancin Farfesa Abubakar Rashid, suka gano jami’o’in da ke gudanar da harkokinsu ba bisa ka’ida ba har guda 49 da suke a wurare daban daban a fadin kasar.

Kamar dai yadda dokar Najeriya ta tanadar duk wata jami’ar da za ta fara yin karatun digiri dole ne sai Gwannatin kasar karkashin jagorancin hukumar kula da harkokin jami’o’I ta kasar ta amince ta kuma bayar da lasisi ga kowace irin jami’a ce kafin ta fara gudanar da aiki.

A bisa wannan dalili ne da hukumar kula da jami’o’in karkashin Farfesa Abubakar Rashid ke jan hankalin daukacin al’umma musamman iyayen yara dalibai da dukkan masu neman yin digiri cewa sakamakon sabawa dokar ilimi CAPE3 ta Tarayyar Nijeriya (2004).a halin yanzu duk an rufe wadannan makarantu da aka lissafa su kamar haka.

Kuma an dauki matakan ne domin Gwannatin ta jaddada kudirinta na ingantawa tare da samar da ilimi mai inganci a kasa baki daya.

Hukumar kula da jami’o’in na shawartar al’umma da su rika kula da matsayin kowace jami’a kafin su yanke hukuncin yin hulda ko fara karatu a cikin ta, domin hakan zai inganta da kuma taimakawa duk mai bukatar neman ilimin kansa ko na yayansa a koda yaushe.

Jami’o’in dai sune;

University of Accountancy and Management Studies

Christians of Charity American

University of Science and Technology

University of Industry

University of Applied Sciences and Management

Blacksmith University

Volta University College

Royal University

Atlanta University

United Christian University

United Nigeria University College

Samuel Ahmadu University

UNESCO University

Saint Augustine’s University of Technology

The International University

Columbus University

Tiu International University

Pebbles University

London External Studies

Pilgrims University

Lobi Business School

West African Christian University

Bolta University College

JBC Seminary Inc. (Wukari Jubilee University)

Kaduna illegal campus Western University

St. Andrews University College

EC-Council USA

Atlas University

Concept College/Universities (London)

Halifax Gateway University

Kingdom of Christ University

Acada University

Filfom University

Houdegbe North American University

Atlantic Intercontinental University

Open International University

Middle Belt University (North Central University)

Lead Way University

Metro University

Southend University

Olympic University

Federal College of Complementary and

Alternative Medicine

Temple University

Irish University Business School

National University of Technology

University of Accountancy and Management Studies

University of Education

Cape Coast University

African University Cooperative Development (AUCD)

Pacific Western University

Evangel University of America and Chudick Management Academic

Enugu State University of Science and Technology

Career Light Resources Centre

University of West Africa

Coastal University

Kaduna Business School

Royal University of Theology

West African Union University

Gospel Missionary Foundation (GMF), Theological University

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.