Home / Labarai / An Gudanar Da Bukuwan Sallah Cikin Kwanciyar Hankali A Jihar Yobe. 

An Gudanar Da Bukuwan Sallah Cikin Kwanciyar Hankali A Jihar Yobe. 

 

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

 

 

An gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali lami  lafiya a fadin jihar Yobe yayin da musulmi suka fito domin gudanar da Sallah Eid-el- Kabir a dukanin masallatai ba tare da fuskantar wata barazanar tsaro ba.

 

 

Wannan biki na Sallah an dai gudanar da shi ne  da karancin matakan tsaro ba kamar yadda aka saba yi a baya ba inda ake tantance masu ibada kafin su isa filin sallar idi.

 

 

Mataimakin gwamnan jihar Yobe Alhaji  Idi Barde Gubana tare da iyalansa da sauran manyan jami’an gwamnati a jihar sun halarci sallar sallar a farfajiyar masallacin dake  cibiyar yada addinin  Musulunci da ke cikin garin Damaturu fadar gwamnatin Jihar.

Babban Limamin Masallacin Yobe ta Cibiyar Musulunci Uztaz Hudu Mohammed ne ya jagoranci Sallar raka’a biyu.

 

 

Ustaz Malam Hudu Muhammad  ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi koyi da darussan Eid-el Kabir amfani wajen inganta soyayya da ‘yan’uwantaka tare da zaman lafiya da juna.

Ya kara da cewa bikin wata dama ce ga musulmi na haduwa tare da taimakawa marasa galihu da ke cikin al’umma.

 

 

“Bikin na yau duka game da sadaukarwa ne da kuma cikakken biyayya ga nufin Allah SWT.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.