Home / Labarai / An kafa Kotun Tafi Da Gidanka Da Za Ta Hukunta Masu Karya Dokar Hana Fita A Kaduna

An kafa Kotun Tafi Da Gidanka Da Za Ta Hukunta Masu Karya Dokar Hana Fita A Kaduna

 Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagoranci  Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i ta samar da kotun ta fi da gidanka da za ta hukunta wadanda ke taka dokar hana fita da aka Sanya a Jihar.
Kamar yadda Gwamnatin Iihar ta fitar da wata sanarwa cewa tuni ma’aikatar shari’ar Jihar ta bayar da umarni ga kotun Majistare da za ta rika zama a wurare daban daban na cikin Jihar domin aiwatar da hukunci ga masu taka dokar.
Indai za a iya tunawa tuni mataimakiyar Gwamnan Dakta Hadiza Balarabe a kwanan baya ta sanar da cewa za ta cire kwanaki biyun da ake bari domin jama’a su damu damar sayen kayan abinci da magani in har aka ki bayar da hadin kai ga dokar.
Kamar yadda babban mai shari’a na Jihar ya bayyana cewa za a rika Yankewa masu karya dokar hukunci ne ba tare da sai an dauke su zuwa kotu ba.
Kamar yadda Umar ya ce tuni aka bayar da umarni ga kotun majistare da za su yi wannan aikin kuma ma’aikatar Shari’ace ta bayar da umarnin.
Kotun za ta rika zama a wurare a cikin birni kamar  Kakuri, Kawo, Magajin Gari, Rigasa, Sabon Tasha, Maraban Rido da Rigachikun kamar yadda ya jaddada.

About andiya

Check Also

DOLE SAI MUN SANYA FASAHAR ZAMANI DON YAƘI DA MATSALAR TSARO -GWAMNA LAWAL GA MAJALISAR ƊINKIN DUNIYA

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada buƙatar amfani da manyan na’urorin zamani domin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.