Home / Labarai / An Kafa Kwamitin Samar Da Ingantaccan Gyara A Kan Aikin Hajji

An Kafa Kwamitin Samar Da Ingantaccan Gyara A Kan Aikin Hajji

Daga Bashir Bello Majalisa Abuja

Dokta Ahmed Adamu Saba, ya bayyana kudirin da aka gabatar a kan batun korafe korafen da aka samu a kan aikin Hajji wanda Malam Muhammad Bi’u ya gabatar da cewa aikin Hajji na shekarar 2024 da aka shirya abubuwa da yawa domin a ba Alhazai amma abin bai yi dai dai ba.

Kamar yadda ya ce mai maganar ya yi maganar Makka da Muna da kuma Madina ba gida mai kyau ba Tanti mai kyau wajen yin tsafta ba kyau akwai kuma wadansu mutanen ma da suka tashi daga Madina suka koma Makka ba su yi kwanan da ya dace ayi a Madina ba ssi suka tashi daga Muna ba su yi kwanan da ya dace ayi ba suka koma Makka, hakika wannan lamarin karin kashe kudi ne duk da irin makudan kudi masu yawa da aka kashe kafin aje aikin Hajjin.

Don haka ne aka gabatar da batun a gaban majalisa saboda wadanda ya dace suke a kwamitin aikin Hajjin su yi doka da hukuncin da ya dace ayi.

” kasancewar hakan ya kawowa Alhazai samun wahala kwarai ba tare da samun abinci mai kyau ba ga kuma ba wurin tsafta mai kyau ayi Bacci ba game da batun motocin da za su dauki Alhazai ma duk ajent ajent da suke da shi a wajen ba su yi aiki mai kyau ba don haka ne ya kawo maganar gaban majalisa kuma majalisar ta amince da batun don haka za a samar da wani kwakkwaran kwamiti da zai yi bincike a cikin lamarin a san yaya za a yi saboda gaba, mu a yadda muka Sani ya zama dole ba wai wadanda kawai ke a nan Najeriya ba za a rika kulawa da su ba kawai har ma wadanda ke wajen Najeriya dole a kula da tsaron lafiya, walwala da jin dadin su a koda yaushe saboda sun je ne da tutar Najeriya duk abin da ya faru ba za a ce wane na kauye Kaza ba sai dai dan Najeriya kawai za a ce saboda haka ne muka zauna muka nada kwamitin da zai yi aiki a kan hakan wato aikin bincike.

Adamu Saba, ya kara da cewa a koda yaushe ana samun karuwar masu tafiya aikin Hajji da kuma an samu yawan mutane za a iya samun damuwa a kan aikin, a saboda haka muke yin kira ga daukacin jama’a da su rika rika duba ainihin kula wa da jin dadi da walwalar jama’a ba wai arzikin da za a samu ba har a samu ingantaccen aikin Hajji

“Saboda haka ne a halin yanzu kwamitin da majalisa ta kafa zai fitar da komai dalla dalla har yadda mutum zai zama ejan na Alhazai daga Najeriya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.