Related Articles
Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna Dakta Hadiza Balarabe, ta bayyana wa al’ummar Jihar cewa ta kara Sanya dokar hana fita da sati biyu.
A cikin sanarwar da ta fitar ta yi godiya ga al’ummar Jihar Kaduna bisa irin yadda suka yi biyayya a kwanaki 60 wato tsawon watanni 2 da aka rika Sanya dokar na kwanaki 30 day biyu.
Kuma sanarwar ta bayyana cewa za a rika fita a halin yanzu na kwanaki uku wato ranakun Talata, Laraba da Alhamis, wato an samu karin kwana daya kenan sabanin da da ake yin kwanaki 2 a sati.
Idan aka duba dai za a ga a cikin sati biyun za a yi kwanaki Takwas kenan cikin Dokar hana fita sauran ranakun kuma za a rika samun walwala.
Wannan sanarwar dai ta biyo bayan karewar kwanaki 30 da Gwamnatin Jihar ta bayyana na dokar a baya.
Sanarwar kuma ta ci gaba da fadakar da jama’a bukatar da ke akwai na yin biyayya ga dokar dakile cutar Covid – 19 da ake kira da Korona bairus.
Da suka hada da a rika wanke hannu, yin amfani da Takunkumin rufe baki da hanci da kuma bayar da tazara tsakanin jama’a tare da kiyaye duk wani taron jama’a.