Home / Labarai / Ba Domin Makarantun Allon Ba Da Gwamnan Bai Iya Karanta Fatiha Ba – Shekarau

Ba Domin Makarantun Allon Ba Da Gwamnan Bai Iya Karanta Fatiha Ba – Shekarau

 Imrana Abdullahi
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa rashin yin kyakkyawan tsari ne ya haifar da halin da makarantun allo suke ciki.
Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ya ce ya ji wani Gwamna daga Arewacin Nijeriya na cewa wai makarantun allon nan ba su tsinanawa kowa komai ba.
Shekarau, ya ci gaba da bayar da amsa cewa ba domin wannan makarantun allon da aka yi tsawon shekaru daruruwa ba da shi wannan Gwamnan na Arewa da bai iya karanta fatiha ba.
“Tsari ne na shekaru da yawa daruruwa da aka yi saboda haka ba zai yuwuba wani ko wasu su zo lokaci daya su ce za su rusa wannan tsarin ba sai dai a hankali kuma sai an yi wa tsarin wani ingantaccen tsari tukuna.
Ya ce ” alokacin da nake Gwamnan Kano hakika na fahimci abubuwa da yawa game da tsarin makarantun allo kuma na yi tsare tsare da dama domin inganta tsarin na kuma samu nasara kwarai”.

About andiya

Check Also

APC SOKOTO FLAGS OFF STATE-WIDE CAMPAIGN IN WAMAKKO LG, UNVEILS 8-POINT AGENDA

  The All Progressives Congress (APC), Sokoto State chapter on Wednesday flagged off its state-wide …

Leave a Reply

Your email address will not be published.