Related Articles
….Burin Mu Kara Inganta Tattalin Arziki Da Ci Gaban Kasa
Daga Imrana Abdullahi
Muktar Ahmad, janaral manaja ne na kamfanin yin Biredi na Zam – Zam da ke Unguwar Tudun Wada cikin garin Kaduna ya jaddada aniyar su ta ci gaba da ingantawa da kyautata sana’arsu ta yin Biredi domin kara bunkasa tattalin arzikin kasa da al’ummarta baki daya.
Muktar Ahmad ya bayyana hakan ne jim kadan bayan karbar lambar karramawar da kungiyar mawallafa jaridu da mujallu ta arewacin Najeriya wato “Arewa Publishers Forum”, suka ba wannan kamfanin Biredi mai albarka sakamakon irin aiki tukurun da suke aiwatarwa.
“Hakika muna matukar farin ciki da kuma kara dankon zumunci a tsakanin wannan kamfani da kuma ku da kuke ganin dacewar irin ayyukan ciyar da kasa da muke yi, muna godiya kwarai”.
Muktar, ” naji kudirin ku lamari ne mai kyau don haka muna godiya kwarai don haka zamu kasance tamkar tsintsiya madaurinki daya tare da ku da ikon Allah don haka mu Kofar mu a bude take a nan gaba koda za a yi wani zama ne da ya shafi Tallafawa al’umma da ikon Allah zamu halarci wurin”.
Muktar ya kuma aike da sako ga daukacin al’umma masu sayen Biredi Zam- Zam da Fantaziyya da cewa duk da irin yadda rayuwa ta kasance ta yi tsada, amma su za su ci gaba da zage damtse wajen ciyar da jama’a da kuma samar da abin yi a tsakanin al’umma kasa baki daya.
“Duk da yanayin tsadar rayuwa wanda a misali idan a can baya zaka iya sayen Biredi kuda daya ya Isa ci a gidanka, amma a yanzu abubuwa sun kara kudi don haka muke ba masu saye su ci hakuri kasancewar muna yin kokari iyakar kokarin mu. Muna sane da cewa koda an kara kudin farashin kaya amma masu gidajen Biredi sai su yi watanni ba su kara wa kowa kudi ba domin taimakawa al’umma kawai domin sana’a ce da ake yi domin taimakon al’umma ba don dan abin da za a samu ba, saboda yanayin al’amuran muke kara ba jama’a hakuri da irin abubuwan da za su gani, mu ingancin kayan mu da muke yi yadda muke yin Biredi nan ba zamu rage komai ba inganci na nan saboda Burin mu shi ne samar da kyakkyawan abinci da nufin inganta rayuwar jama’a baki daya”.