An Karyata Zargin Da Ake Wa Kungiyar TOAN
Imrana Abdullahi
Shugabannin kungiyar masu Baburan haya masu kafa uku da ake kira “TOAN” reshen Jihar Kaduna sun Karyata zargin da ake yadawa cewa wai suna buga rasidin da suke Sayarwa yayan kungiyar a dukkan tashoshin da ake daukar fadinja.
Sakataren kula da ayyukan Jin dadi da walwalar jama’a na kungiyar reshen Jihar Kaduna, Mahadi Lawal ne ya Karyata zargin lokacin da yake ganawa da manema labarai a Ofishin kungiyar da ke Bakin ruwa Kaduna.
Mahadi Lawal ya tabbatarwa da manema labarai cewa hakika wannan rasidin da suke Sayarwa na Gwamnati ne kuma an yi zama da shugabannin kananan hukumomi kafin a dawo da sayar da wannan rasidi ga yayan kungiyar don haka jama’a kada su amince da duk wata magana sabanin irin abin da ya fito daga bakin shugabannin kungiyar TOAN na Jiha.
“Hakika mu muna yin biyayya ga Gwamnatin Jihar Kaduna bisa tsare tsaren da take aiwatarwa domin ciyar da Jihar Gaba, don haka ya yi kira ga daukacin yayan kungiyar masu Kekunan haya masu kafa uku “TOAN” da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwamnatin Jihar Kaduna domin samun kwalliya ta biya kudin sabulu”.
Kwamared Mahadi Lawal ya kuma nunawa manema labarai irin residan da ake Sayarwa yayan kungiyar direbobin da suke tuka Baburan masu kafa uku domin tabbatar da sahihancin maganar da yake fadi.
Ya kuma yi godiya ga Gwamnatin Jihar Kaduna bisa matakin da ta dauka na yin Fenti ga dukkan Babura masu kafa uku domin kamar yadda Kwamared Mahadi Lawal ya shaidawa manema labarai cewa tsarin na taimakawa wajen daurin gano duk wani direba da ya aikata wani abu ko aka samu matsalar bacewar kaya nan da nan za a iya ganin kayan cikin Sauri kuma a kawo ma kungiyarsu ta TOAN inda ya nuna wa manema labarai irin tarin kayan jama’a da suka mance da su a cikin Babura masu kafa uku da suka hau a matsayin fasinjoji kuma suna neman masu kayan a halin yanzu.
Sai dai Kwamared Mahadi Lawal ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i da ta taimaka wajen samawa yayan kungiyarsu karin Babura masu kafa uku domin kamar yadda ya ce akwai dimbin matasa da suke bukatar samun abin yi, saboda haka idan Gwamnati ta duba matsalar ta su suna ci gaba da yin godiya kwarai domin taimakawa mutum daya taimakon al’umma ne da yawa.
Manema Labaran sun kuma samu tabbacin cewa kafin a dawo da sayar da rasidin ga masu Babura masu kafa uku bayan watanni uku da Gwamnatin ta ba su domin samun sauki ga batun matsalar cutar Korona, sai da aka zauna taro a gidan Gwamnati da shugabannin kungiyar, shugabanni a bangaren Gwamnati da suka hada har da na hukumar tara kudin haraji da shugabannin kananan hukumomi domin a cimma nasarar gudanar da aikin