Daga Imrana Kaduna
Kamar yadda rahotannin da muke samu da yammacin nan ke cewa Gwamnatin Jihar Nasarawa ta mayar da tsohon sarkin Kano da aka sauke a jiya garin Awe a karamar hukumar Awe cikin Jihar Nasarawa a arewacin tarayyar Nijeriya.
Kamar yadda rahotannin suka bayyana wa majiyar mu cewa gidan da aka kai tsohon sarkin Sarkin shugaban karamar hukuma ne.
Dama an jiyo sarkinnLoko inda aka kai tsohon Sarkin Kano tun da farko na cewa garin Loko a gaskiya kauye ne.
Wadanda suka raka shi cikin sabon gidan nasa akwai Sarkin lafiya Sidi Bage da kuma sarkin Awe Isa Umar na II.
Abubakar Ahmad Sabo Loko, shi ne mai martaba Sarkin Loko a Jihar Nasarawa da ke Arewacin tarayyar Nieriya ya bayyana “wurin da aka kai tsohon sarkin Kano Alhaji Sanusi Lamido Sanusi a matsayin kauye”.
Mai martaba sarkin na Loko ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta muryar Amurka Sashen hausa, inda ya ce Loko nan ne aka ajiye tsohon sarkin Gwandu Almustapha Haruna Jokolo lokacin da aka cire shi daga sarautar Gwandu.
Saboda haka ya ce wurin nan hakika kauye ne don haka yana da kyau a san haka, saboda haka koda shi tsohon Sarki haruna Jokolo sai daga baya aka mayar da shi Kaduna.
Sai ya yi kira ga daukacin wadanda keda iko a kan wannan lamarin da su san cewa wurin fa wato Loko kauye ne.