Home / Labarai / An Rushe Ginin Da Za A Yi Taron Yin Zina A Kaduna

An Rushe Ginin Da Za A Yi Taron Yin Zina A Kaduna

An Rushe Ginin Da Za A Yi Taron Yin Zina A Kaduna
Mustapha Imrana Andullahi

Jami’an ma’aikatar kulawa da ingancin gine gine KASUPDA ta Jihar Kaduna sun rushe wani katafaren ginin da aka shirya yin taron gangamin fatin yi Zina a Kaduna.

 

Mai magana da yawun hukumar, Nuhu Garba Garba shaidawa manema labarai a Kaduna cewa ginin wanda yake a unguwar Sabon Tasha Tasha wani yanki na garin Kaduna an rushe shi ne a Yammacin yau Laraba.

 

Ya ci gaba da cewa rushe ginin ya faru ne bisa duba da dokar da ta kafa hukumar.

 

“ Dokar ta bayar da iko ga hukumar ta rushe duk wani gini da ya sabawa tsarin da aka tanadar ko ya takurawa mazauna wurin.

 

“ A misali idan aka mayar da gini sabanin abin da ake nufin yi da shi tun farko, dokar ta bayar da karfi ga hukumar ta rushe shi baki daya musamman in ya sabawa abin da jama’a suke bukata wato ya takara su”.

 

Garba  Ya kara da cewa ” muna a unguwar Narayi ( wani wuri daban) domin aiwatar da aiki makamancin wannan. Muna rushe wani ginin da yake bayar da kara inganta harkokin shan miyagun kwayoyi”.

 

Mun dai samu labarin cewa batun rushe wannan gini da aka yi gangamin yin taron Badala (zina) a kalla awanni 24 da kama wadanda ke kokarin yin gangamin.

 

Wata majiya dai ta shaidawa jaridar mu ta yanar Gizo cewa an dai kama mutanen ne a ranar Laraba da Alhamis.

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.