Related Articles
An Saki Malami Da Matarsa Da Yan Bindiga Suka Sace A Kaduna
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa an sami nasarar kubutar da Malamin addinin Kirista Emmanuel Ego Bako da aka sace a ranar Juma’a da Yamma tare da matarsa Cindy Bako da aka sace.
Shi dai Malamin addinin tare da matarsa an sace su ne a ranar Juma’a da Yamma a wurin addu’a na Albarka da ke kan titin Afana – Fadan Kagoma – Kwoi a karamar hukumar Jema’a.
Sakataren Cocin Fetakostal (PFN) da ke Kaduna Rabaran Tony Iwulale ne ya tabbatar da hakan ga Gwamnatin Jihar Kaduna.
Duk bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan ya sanyawa hannu.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I ya bayyana cikakkiyar gamsuwarsa tare da farin cikin jin wannan labarin inda ya jajantawa Malamin addinin tare da matarsa.