Home / Labarai / An Saki Malami Da Matarsa Da Yan Bindiga Suka Sace  A Kaduna

An Saki Malami Da Matarsa Da Yan Bindiga Suka Sace  A Kaduna

An Saki Malami Da Matarsa Da Yan Bindiga Suka Sace  A Kaduna
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa an sami nasarar kubutar da Malamin addinin Kirista Emmanuel Ego Bako da aka sace a ranar Juma’a da Yamma tare da matarsa Cindy Bako da aka sace.
Shi dai Malamin addinin tare da matarsa  an sace su ne a ranar Juma’a da Yamma a wurin addu’a na Albarka da ke kan titin Afana – Fadan Kagoma – Kwoi a karamar hukumar Jema’a.
Sakataren Cocin Fetakostal (PFN) da ke Kaduna Rabaran Tony Iwulale ne ya tabbatar da hakan ga Gwamnatin Jihar Kaduna.
Duk bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan ya sanyawa hannu.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I ya bayyana cikakkiyar gamsuwarsa tare da farin cikin jin wannan labarin inda ya jajantawa Malamin addinin tare da matarsa.

About andiya

Check Also

Our Mandate Is To Organise Congresses, Says Labour Party Transition Committee Chairman, Umar

  Former president of the Nigerian Labour Congress, NLC, and Transition Committee chairman of the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.