Home / Labarai / An Samu Rarar Naira Miliyan Sama Da Dari 470 Na Ma’aikatan Bogi A Sakkwato – Tambuwal

An Samu Rarar Naira Miliyan Sama Da Dari 470 Na Ma’aikatan Bogi A Sakkwato – Tambuwal

An Samu Rarar Naira Miliyan Sama Da Miliyan Dari 470 Na Ma’aikatan Bogi A Sakkwato – Tambuwal

Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa sakamakon umarnin da ya bayar na a bincika tare da tantance ma’aikatan Jihar Sakkwato an samo rarar kudi sama da naira miliyan dari 470.
Gwamnan ya bayyana cewa shi da kansa ne ya bayar da wannan umarni na bincika ma’aikatan bogi domin tace bangaren aikin Gwamnati.
“Kuma na bayar da umarnin a ci gaba da wannan aikin zuwa matakin kananan hukumomi baki daya”, inji Shi.
Ya kara da cewa wadanda aka samu da wannan laifi suna nan ana tuhumarsu kuma za a gabatar da su gaban kuliya.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya dai bayyana hakan ne a wani shirin tattaunawar da aka yi da shi na gidan rediyon bbc hausa wanda aka dauki nauyi na hadin Gwiwa da cibiyar Maccather da aka dauki shirin a garin Abuja.
Gwamna Tambuwal ya kuma bayyana cewa dukkan matakin da za a dauka domin inganta lamarin gudanar da zabe a Nijeriya yana goyon bayansu.
Ya ce tuni aka aikewa majalisar dokokin Jihar Sakkwato sunayen wadanda za su jagoranci hukumar zabe ta Jihar Sakkwato kuma an tantancesu don haka ana shirye shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi a Jihar.
Sai dai ya ce daga cikin abin da ya hana yin zabe a Jihar akwai yanayin siyasa da aka shiga da kuma batun kudi, amma ya tabbatar da cewa za a yi zaben cikin yardar Allah.
A game da batun inda suke fama da zaizayar kass kuwa ya ce akwai wani tsarin hadin Gwiwa tsakanin Gwamnatin Jihar Sakkwato da wata hukumar kula da irin wadannan matsaloli da ake cewa NEWMAPP, wanda Gwamnatin Jihar Sakkwato tuni ta bayar da nata kason kudi domin yin aikin da suka kai naira biliyan uku a shekaru uku da suka gabata, amma its wannan hukuma bata Sanya nata kudin a asusun ba domin cika alkawari a bayar da aikin.
” Kwanan nan na yi magana da babban jami’in kula da aikin a ita hukumar da za mu yi aikin hadin Gwiwa kuma ya tabbatar mana da cewa nan bada jimawa ba za a samu gagarumin ci gaba a lamarin wato za a bayar da aikin.
Gwamna Tambuwal yasha tambayoyi daga dimbin jama’a a fannonin aiki da gudanar da Gwamnati kuma duk ya samu nasarar amsa tambayoyin harma ya kan cewa jama’a suje su ganewa idanunsu maganin tambaya, inda ake da zargi ya cewa jama’a su gaya masa wurin da matsalar take domin gudanar da bincike sosai.

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.