Related Articles
..Za A Yi Wa Kowa Adalci A KASUPDA
Daga Imrana Abdullahi
A kokarin da Gwamnatin Jihar Kaduna ke yi karkashin jagorancin Gwamna Sanata Kwamared Uba Sani domin ganin an warware tare da sharewa jama’a Hawayensu musamman a game da wadanda ke kokarin yin ginin Gidaje a Kaduna a halin yanzu dai za a iya cewa an samu sabuwar hukumar bayar da izinin yin ginin Gudaje karkashin Kwararren injiniyan ginin Gudaje Dokta Abdurrahman Yahya a matsayin Darakta Janar kuma shugaban KASUPDA.
Kamar dai yadda kowa ya Sani an yi ta samun wadansu korafe korafen matsalar samun izinin hukumar KASUPDA domin jama’a su fara gina filayensu da suka mallaka, amma sai ayi ta samu matsaloli nan da can ya sa sabon shugaban hukumar Dokta Abdurrahman Yahya ya shigo da wani kyakkyawan tsarin kiran jama’a domin a saurari korafin da suke da shi musamman ma a bangaren samun izinin yin gine ginen gidaje, Makarantu, Asibitoci da kuma wuraren sayar da abinci da dai sauran harkar yin gini a Jihar.
Dokta Abdurrahman Yahya ya dai fitar da tsarin a kowane wata Uku za a yi a kalla kwanaki hudu ana zaman sauraren jin korafe korafen jama’a daga ko’ina suke a duk fadin jihar.
Hakika za a iya cewa wannan tsarin sauraren jama’a da aka fito da shi a wannan zamanin Gwamnatin Jiha karkashin Sanata Uba Sani da ya damka aikin a hannun masanin harkar Gine gine Abdurrahman Yahya da wadansu ke yi wa lakabi da jagoran tabbatar da zaman lafiya, kasancewar wasu jama’a sun shiga cikin wani hali dalilin kokarin da suke yi na tabbatar da sun gina muhalli, Makarantu, Asibitoci, Wuraren cin abinci da dai sauran gine gine da dama domin gudanar da rayuwar dan Adam.
An dai fara wannan shirin jin korafe korafen jama’ar ne a ranar Litinin da ta gabata kuma an samu halartar jama’a daga garin Kafanchan, Zariya da kuma cikin garin Kaduna da suka fito fili a gaban jama’ar da suka taru a dakin taron hukumar bayar da izinin gina gidaje ta Jihar Kaduna.
Kai in dai baku bayani wadansu mutanen da suka zo bayar da korafinsu har kuka suke yi sakamakon murna da farin ciki domin kawai an ba su damar bayyana korafinsu a gaban shugaban hukumar KASUPDA tare da jagirorin hukumar da kuma manema labaran da suka halarci wurin
Kamar yadda wani da ya gabatar da korafin nasa ya shaidawa manema labarai tun a ranar farko cewa hakika ya ji dadi kwarai da ya samu yin magana ya gabatar da korafinsa a gaban shugaban hukumar KASUPDA kuma zai je ya shaidawa duk wani mai korafi cewa yazo ga dama ta samu domin ayi masa maganin matsalarsa da ta shafi batun yin gini da yake yi ko ya yi ko yake kokarin aiwatarwa.
Kadan dai daga cikin irin korafe korafen da aka gabatar sun hada da batun samun izinin fara yin gini ko kuma batun wasu da suka yi ginin kafin su samu takardar fara yin ginin duk da wani ya ce masa ya ci gaba da yin gininsa ko ba tare da takardar izinin ba.
Kuma da jin wadannan korafe korafe shugaban hukumar ta KASUPDA Dokta Abdurrahman Yahya ya tabbatarwa da za a yi wa kowa adalci a game da korafin da ya gabatar.
Masanin harkokin yin gine gine kuma shugaban hukumar KASUPDA Dokta Abdurrahman Yahya ya kuma yi gargadi da kakkausan murya tare da jan hankali ga dukkan ma’aikatan hukumar da kada wanda ya saka kansa a harkar batun Filaye domin ba aikin hukumar ba ne.
Dukkanin wadanda suka halarci zaman suka gabatar da korafinsu suna bayyana farin ciki da jin dadin irin damar da suka samu wanda sakamakon hakan suke yi wa shugaba Abdurrahman Yahya addu’ar Allah ya saka masa da alkairi ya yi masa jagora ya kuma kara masa dimbin basirar kula wa da harkokin jama’a ta yadda Jihar Kaduna da kasa baki daya za su ci gaba.
Za dai mu rika kawo maku idan hali ya yi irin yadda zaman jin korafe korafen jama’ar ya gabata a nan gaba
Kuma irin wannan zama za a rika yin da ne a duk bayan watanni uku domin a samu gyara da dai daito a tsakanin al’umma.