Daga Imrana A Kaduna
Majalisar Zartaswar Jihar Kano ta amince da sauke Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi Lamido Sanusi daga sarautar, a wani zama na musamman da majalisar ta yi a ranar Litinin.
Kafin dai cire shi akwai lamarin tayar da cibiyoyin wuta a majalisar dokokin Jihar game da lamarin a ranar Litinin.
Lokacin rubuta wannan labarin tuni aka girke jami’an tsaro a majalisar.
Kamar yadda lamarin ya kasance a majalisar an samu tayar da hakarkari lokacin mahawara game da rahoton da shugaban hukumar sauraren korarin jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta ta Jihar kano.