Home / Labarai / An Tabbatar Da Gaskiya, Adalci A Jihar Kaduna – Shehu Bakauye

An Tabbatar Da Gaskiya, Adalci A Jihar Kaduna – Shehu Bakauye

Mustapha Imrana Abdullahi
Dan majalisar wakilai ta tarayyar mai wakiltar kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari, honarabul Shehu Balarabe da ake yi wa lakabi da Bakauye, ya bayyana cewa a iya saninsa an tabbatar da yin zabe cikin gaskiya da adalci a zaben shugabannin mazabu a Jihar Kaduna.
Honarabul Shehu Balarabe ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Kaduna.
Balarabe ya ce a iya saninsa karkashin jagorancin Gwamna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I an tabbatar da yin zaben adalci tun daga lokacin da aka amincewa kowa ya sa yi takardar tsayawa neman kujerar jagorancin jam’iyya a matakin mazabu, sabanin a wasu Jihohin da kawai ba a Sayarwa da mutane takardun tsayawa takarar ba”. Inji shehu Balarabe.
Sai dai dan majalisar na tarayya Shehu Bakauye, ya ce shi bai san batun sakin layi na kaza ko kaza ba tun da shi ba Lauya ba ne amma dai “na san an tabbatar da gaskiya da yin adalci ga kowa ne mutum da ke kokarin tsayawa takara”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.