Home / Big News / An Tsinci Gawar Magidanci A Bakin Rafi a Karamar Hukumar Sanga

An Tsinci Gawar Magidanci A Bakin Rafi a Karamar Hukumar Sanga

Daga Muhammad Sanusi Abdullahi

An tsinci gawar wani magidanci xan kimanin shekara sittin da biyar mai suna Danjuma Bako, yashe a bakin rafi a qaramar hukumar Sanga da ke kudancin jihar Kaduna.

Magidancin, xan asalin qauyen Kiban da ke gundumar Gwantu, an ce ya zarce zuwa wani jana’iza ne na wani dan uwansa da misalin karfe hudu na yammacin lahadi daga gonarsa inda ba a qara jin duriyarsa ba tun daga nan.

An ce bayan jiran tsammani daga danginsa ne washegari litinin suka fita nemansa inda su ka ci karo da gawarsa qasa ta rufe gefen jikinsa a bakin rafi.

Wani mazaunin garin da ya bukaci a sakaye sunasa yace marigayin ya tafi jana’izar dan uwansa ne da shi ma wasu mahara suka kashe a Unguwan Anjo da ke karamar hukumar Jama’a da ke makwabtaka da su.

Yayinda Garkuwa ta tuntubi shugaban karamar hukumar Sanga, Mista Charles Danladi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana damuwarsa kan karuwar kashe-kashe a yankin.

Yace dole sai jami’an tsaro sun tashi tsaye don ganin sun shawo kan wannan matsalar da taki ci taki cinyewa.

Shugaban karamar hukumar ya kara da cewa a kwanan nan ma wasu matasa sun kama wata yarinya ‘yar kauyen Anka amma mazauniyar Abuja bayan ta kawo ziyara ga fitaccen xan siyasar yankin, Ishaya Abu Anka, inda su kayi mata fyaxe.

About andiya

Check Also

Gwamna Radda Ya Koka Da Cewa  22 LGAs Marasa lafiya A Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Dakta Dikko Umar Radda ya koka kan matsalar tsaro a jihar Katsina, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.