Related Articles
MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
An bayyana kasashen al’ummar musulmi da cewa sun kasance a cikin jarabawa matuka da gaske don haka a dage da yin addu’o’i a wuraren yin Sallah da sujada da kuma cikin Dare kasancewar halin da ake ciki a yanzu ya fi karfi kowa
Malam Ibrahim Rafin Gomo ne ya bayyana hakan a wajen tafsirin watan Ramadana na Bana a masallacin ‘Choice plaza’ da ke Kaduna.
Idan an yi hakuri hakika taimakon Allah na kusa domin tun da Allah ya halicci duniya akwai jarabawa.
“Duniya ba za ta tashi ba sai an ga abubuwa daban daban, don haka mu koma ga Allah mu kuma kaskantar da kai, Allah ya sa mu dace”.
Malam Ibrahim ya kuma Fadakar da jama’a su rika duba wa sosai a wuraren ibada da dukkan wuraren taruwar jama’a don kiyaye wa da tabbatar da tsaro.
“Kuma dukkan masu mulki lallai su tabbatar Allah zai taimbaye su na shugabancin da aka ba su”.
“Duk wanda ya rike gaskiya za ta yi masa jagora zuwa gidan Aljannah, don haka kowa ya dage Gwargwado”.
An gargadi daukacin al’umma su gujewa girman kai,hassada da kyashin Juna a koda yaushe don haka a duk lokacin da Allah ya ba wani ni’ima ko daukaka to sai a bishi kawai a mika wuya, musulmai su zama masu basira ban da damuwa da jin zafin juna
Malam Ibrahim Rafin Gomo ya kuma tabbatar da cewa Rashin amincewa da abin da Allah ya hukunta na kawo matsaloli a cikin kasa don haka sai ayi hattara.