Home / Lafiya / An Yi Kira Ga Mata Su Rika Kai Yayansu Rigakafi – Hamza Ibrahim Ikara

An Yi Kira Ga Mata Su Rika Kai Yayansu Rigakafi – Hamza Ibrahim Ikara

Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban hukumar kula da lafiya matakin farko na Jihar Kaduna Hamza Ibrahim Ikara, ya yi kira ga daukacin iyaye mata da su rika kai yayansu allurar rigakafi.
Hamza Ibrahim Ikara ya yi wannan kiran ne a wajen babban taron kaddamar da fara yi wa yara allurar rigakafi a dukkan fadin kananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna da aka yi a cikin garin Kaduna.
Hamza Ibrahim Ikara ya ci gaba da bayanin cewa ya dace iyaye maza su ga ne cewa abu ne mai matukar muhimmanci su rika barin matansu domin su kai yaransu wuraren da ake yin allurar rigakafi da nufin samun ingantacciyar al’umma
Ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Kaduna da su ci gaba da bayar da hadin kai da goyon baya ga dukkan shirye shiryen Gwamnati domin yin maganin cutar Korona da ta addabi duniya.
Hamza Ikara ya ce za a yi wannan tsarin Rigakafin ne kashi biyu na farko za a yi kwanaki shida (6) sai kuma zagaye na biyu shima kwanaki shida (6) wato dai za a yi tsawon kwanaki Goma sha biyu ana yin wannan Rigakafin tuttukan Bakon dauro, Cutar Shan’inna da wasu cututtuka masu addabar kananan yara da kuma yi wa jama’a Gwajin Korona domin ba su katin shaidar cewa ba su dauke da cutar.
Sai dai Hamza Ikara ya ce za a ci gaba da Gwajin cutar Korona har zuwa nan gaba don haka ake kira ga jama’a su bayar da hadin kai da goyon baya.

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.