Home / Labarai / An Yi Rashin Babban Gwarzo Mai Kishin Kasa – Ramalan Yero

An Yi Rashin Babban Gwarzo Mai Kishin Kasa – Ramalan Yero

An Yi Rashin Babban Gwarzo Mai Kishin Kasa – Ramalan Yero
Mustapha Imrana Abdullahi
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Muktar Ramalan Yero ( Dallatun Zazzau)  ya bayyana rasuwar tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Abdulkadir Balarabe Musa a matsayin wani babban rashin da zai yi wahalar cikewa.
Tsohon Gwamna Mukatar Ramalan Yero Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala Sallar Jana’izar tsohon Gwamna Balarabe Musa a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.
Ramalan Yero ya ce marigayin mutum ne mai hakuri da tsananin gudun duniya ga karrama jama’a tare da yin fafutuka domin tabbatar da adalci a tsakanin jama’a a koda yaushe.
“Shi kowa nasa ne indai mutum zai tsare gaskiya da amana babu nuna wani bambanci ko kadan”.
Da yake tofa albarkacin bakinsa jim kadan bayan kammala Sallar Jana’izar shugaban jam’iyyar Labour na Jihar Kaduna Alhaji Umar Taba Mai Rakumi bayyana rashin Balarabe Musa ya yi da cewa sai shugabannin yankin arewa sun yi da gaske kafin su samo wanda zai cike gurbin tsohon Gwamnan Balarabe Musa, musamman domin irin ingancinsa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.