Home / Labarai / An Yi Taron Fadakarwa Ga Malamai Da Limamai A Jihar Kaduna

An Yi Taron Fadakarwa Ga Malamai Da Limamai A Jihar Kaduna

 

 

 

Daga Imrana Abdullahi

 

An yi kira ga daukacin malamai masu yin wa’azi da su fara da sanin manufar abin da ya sa suke yin wa’azi domin cimma Burin da ake bukata na samun ci gaba.

Farfesa Yahaya Mijahid ne ya yi wannan kiran a wajen taron Limamai da Malamai da aka yi a dakin taro na jama’atunnasarul Islam hedikwata Kaduna.

Farfesa Mujahid ya ci gaba da cewa duk wanda ba shi da manufa hakika ba zai cimma bukatar da ta dace a samu ba a wajen gudanar da duk wani wa’azin da ake yi.

Farfesa Mujahid ya kuma ja hankalin malamai a lokacin wa’azi da su kaucewa tsayawa kan mayar da martani kawai a madadin yin wa’azi ga al’umma

Mujahid, ya kara jaddada cewa harkar musulunci daban da kuma wani addini can da ba na musulunci ba

Ya yi kira ga majalisar malamai da Limamai da su fitar wa da malamai wadansu mauru’an da za a yi maganganu a kansu domin a samu cikakken saitin yin wa’azi.

An kuma yi kira ga majalisar malamai da Limamai da su rika bibiyar irin yadda masu wa’azi ke gudanar da ayyukansu da nufin samun kyakkyawar nasarar da ake bukata

Dokta Yusuf Arrigasiyyu, ya ce a nan da bayan Azumi za a kaddamar da majalisar a kowace kananan hukumomi da nufin samun ciyar da addinin Islama gaba ta hanyar samun hadin kai a tsakanin al’umma

Dokta Rigasiyyu ya kuma yi kira ga masu wa’azi da su mayar da hankali a kan a rika yin taimakekeniya a tsakanin Juna musamman a wajen ciyarwa tsakanin Juna, kasancewar a halin yanzu ana cikin wani hali na maganar abinci

Ya kuma yi magana a kan halin da malamai ke ciki, saboda haka a rika kula da batun halayyar wasu malamai hakika na bukatar gyara.

Malamai su rika kula da kansu musamman a wajen neman abin duniya a hannun wasu mawadata da ke cikin al’umma.

A wajen babban taron Malamai da Limaman an yi kira da fadakarwa a kan irin yadda kowa ya dace ya aiwatar da wa’azi musamman a lokacin Azumin watan Ramadana mai zuwa

An fadakar a kan ka’idojin da ya dace mai yin wa’azi ya Sani kafin ya zama mai hawa kan mumbarin wa’azi da nufin amfanin al’umma baki daya.

 

A wajen taron Shaikh Faisal Badani ya yi wa mahalarta taron jawabi game da bukatar da ake da ita na gujewa masu ruruta wutar ayi Zanga Zanga ga Gwamnati inda ya bayar da misali da irin abin da ke faruwa a halin yanzu a kasar Sudan wanda ya ce lamarin ba dadi ko kadan.

 

Dimbin malamai da Limamai ne suka halarci taron daga kananan hukumomin Jihar Kaduna da nufin a saita yadda ya dace ayi wa’azin watan Ramadana mai zuwa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.