Home / News / Ayyukan ta’addanci da kauce ma gaskiya da akeyi – Yusuf Dingyadi

Ayyukan ta’addanci da kauce ma gaskiya da akeyi – Yusuf Dingyadi

Wannan rashin imani na ci gaba da kai hare -haren ta’addanci a wasu garuruwan yankin gabashin Sakkwato yana cike da ban takaici da tausayi.
Harin da aka kai a wasu kauyukan Goronyo a jiya abin yayi muni matuka, haka ma da irin na Sabon Birni, Isa, Rabah da Gwadabawa da wasu kauyukan Kware a kwanaki baya.
Yana da kyau yan Majalisun Tarayya dake Abuja su aje shan shayi da manyan hafsoshin tsaro ko daukar hotuna ziyara garesu; suyi watsi da wadanan alkawulan da suke masu, marasa nasara da amfani.. lokaci yayi da zasu hada kai baki dayansu, don fuskantar shugaban kasa kai tsaye, tare da neman ya sanya baki akan wannan matsalar, don kuwa TURA TA KAI BANGO!
Lamarin barazana tsaron nan a jahar mu ya wuce siyasa ko jam’iyya, mun fadi haka a baya, lokaci yayi da zamu yarda da abin da yafi alfanu ga al’umma ba tsayawa muna jiran ayi mana ba ko aza laifi akan wani ko gungun wasu da basu iya magance shi.
Ga fili ta nuna irin matakan da tsohon Gwamna Tambuwal ya dauka da wadanda Gwamna Ahmed Aliyu yake dauka a yanzu akan lamarin nan na tsaro ba zasu iya shawo kan karshen wannan matsalar ba kacokan; dole ne sai har an samo tallafi na kwarai daga Abuja, tare da gina manyan barikokin soja da na yan sanda tare da samar da issasun kayan aiki irin na zamani don kai agajin gaggawa tare da fuskanta yan ta’adda har wuraren da suke cin kasuwarsu.
Yan ta’adda nan fa suna nan a cikin mu, tare da aiki da ‘Informants ‘ da kuma hada baki da wasu baragurbin jami’an tsaro dake basu bayanai ko kayan aiki na makamai da suke kai farmaki akan al’umma.
Mu aje siyasa, mu rungumi gaskiya akan yaki da ta’addanci don ceto al’ummar yankin gabashin Sakkwato da ma sauran wuraren dake fuskanta barazana.
Wannan dauki daya bayan daya da ake yiwa al’umma a cikin kauyuka da birane yayi illa, yana da hatsari kuma bala’i ne mai yawa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali na jama’ar jahar Sokoto baki daya da ma kasa Najeriya.
Allah Ya kawo mana mafita
Yusuf_Dingyadi ne ya rubuto wannan sharhin

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.