Home / Garkuwa / Ba A Harbe Ni Ba, Ina Cikin Koshin Lafiya, Inji Wanda Ake Cewa Ya Kaiwa Buhari Hari A Arugungu

Ba A Harbe Ni Ba, Ina Cikin Koshin Lafiya, Inji Wanda Ake Cewa Ya Kaiwa Buhari Hari A Arugungu

Daga Bashir Rabe Mani A Birnin Kebbi
Jamilu Guddare, shi ne wanda ake ta yada zargin wai ya kaiwa shugaba M7hammadu Buhari, hari a garin Arugungu Jihar Kebbi a ranar Alhamis.
Jamilu Guddare, ya ce babu wanda ya harbe shi don haka yana cikin kishin lafiya tare da kwanciyar hankali.
Jamilu wanda ya yi karatunsa a jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato ya shaidawa manema a gidan Gwamnatin Jihar Kebbi, a ranar Juma’a cewa ya dauki aniyar gaisawa da shugaba Muhammadu Buhari, domin kawai ya gaishe shi.
Guddare ya tabbatar da cewa ” hakika wannan rana shi a wajensa ta tarihi ce domin da dadewa na matsu da in ga shugaba Buhari domin mu gaisa hannu da hannu.
“Saboda irin kokarinsa na gudanar da mulkin adalci tare da tsare gaskiya da Amana, don haka koda an harbe ni na mutu na cimma Burina da na dade ina matan gani in ga Buhari a matsayina na mutum”.
“Wannan mutum ne da kasance ministan Fetur, kuma Gwamnan mulkin soja, shugaban hukumar tara rarar kudin man fetur, kuma tun daga shekarar 2015 zuwa yanzu shi ne shugaban kasa, duk da haka har yanzu bai yi wa arzikin kasa wawaso ko rikon wasarairai da dukiya ko arzikin Nijeriya ba”.
Sai dai Guddare ya mika sakon ban hakuri ga shugaba M7hammadu Buhari, Gwamna Atiku Bagudu da daukacin yan Nijeriya, game da irin matakin da ya dauka mai cike da hadari inda ya tabbatar da cewa ya saba wa tsari da ka’ida.
Guddare ya ci gaba da cewa babu wanda ya yi masa azaba kamar yadda wadansu mutane suke yadawa ba duk ba haka abin yake ba cewa wai jami’an tsaron DSS sun yi masa azaba, “An rike ni da martaba da mutunci na ci na sha hani an”.
 Da yake jawabi, ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed cewa ya yi dukkan rahotannin da ake yadawa game da faruwar wannan lamari cewa wai an kai wa shugaba Buhari hari duk karya ne domin ba su da tushe balantana makama.
“Jamilu Masoyin shugaba Buhari ne, don haka dukkan rahotannin cewa an kai wa Buhari hari karya ne, ya yi kokarin ya ga Buhari ne ya gaisa da shi kuma ba a harbe shi ba, Lamar yadda wasu ke yadawa”.
Da yake nasa jawabin Gwamna Atiku Bagudu, alkawari ya yi na cewa za su hadu da ministan yada labarai domin isar da sakon Guddare ga Buhari yana mai cewa ” Kuma zamu yi kokarin shirya taron tattaunawarsu da Shugaba Buhari domin su gana da Guddare”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.