Daga Imrana Abdullahi
Yusuf Iliyasu da ya ne daga cikin amintattun kungiyar masu harkar Gwangwani da ake cewa Jari Bola ko masu sharar karfe da duk wata kazanta domin kiyaye muhalli da kuma samar da ayyukan yi ga dimbin matasa a cikin al’umma ya tabbatarwa da duniya cewa ba su da wani batagari a cikin hadaddiyar kungiyarsu ta (NASWDEN).
Yusuf Iliyasu Iliyasu ake yi wa lakabi da trusty” ya bayyana wa manema labarai hakan ne Jim kadan bayan an Rantsar da shugabannin kungiyar ta kasa reshen Jihar kaduna da kuma na shiyya da suka fito daga Jihohi a wajen wani taron da aka yi a Kaduna.
Yusuf ya ce ” hakika a cikin wannan kungiya ta su sam ba su da wani batagari kuma duk inda suka samu wadanda suka yi masu kutse sukan hannanta su ga hukuma domin a dauki matakin da ya dace da su.
Ya ce a kokarin da suke na mayar da ababen da ake gani kamar ba su da amfani su zama masu yin amfani lallai suna kokari ne domin ciyar da tattalin arzikin kasa gaba, kasancewar akwai dimbin abubuwan da har yanzu ba a fara ma amfana da su ba a cikin Najeriya sabanin wadansu kasashen duniya da tuni har sun ci gaba a fannoni daban daban na sarrafa abubuwa da dama ta yadda jama’a za su amfana.
A game da sababbin shugabannin da aka Rantsar tare da ba su shahadar kama aiki kuwa, ya taya su murna da kuma fadakar da su cewa su Sani lallai wannan wani nauyi ne aka Dora masu na yin shugabanci, ina yi masu addu’ar Allah ya Sanya su sauke nauyin da aka Dora masu da izinin ubangiji.
“Sana’ar Gwangwan ta na samawa matasa aikin yi kuma ba wai a nan kadai ba, akwai wadansu abubuwan da har yanzu ba a kai ga ana sake sarrafa su ba amma wasu kasashe tuni sun wuce da hakan, sannan sana’ace mai kokarin gyara duk wani gurbatacce idan mai gyaruwa ne. Kowace sana’a a kan samu batagari amma dai muna yin kokari muga cewa duk mun nisanta kan mu daga batagari, masu zuwa suna Rabe wa tare da mu ba fa tare da mu suke ba riga ce kawai suke shigowa kuma a duk lokacin da muka samu labari ko wani sahihin bayani a game da irinsu muna daukar mataki domin a yi maganinsu ba tare da bata lokaci ba.