Home / News / BA WANDA ZAI CIRE BOLA TINUBU DAGA MULKIN NAJERIYA – INJINIYA KAILANI

BA WANDA ZAI CIRE BOLA TINUBU DAGA MULKIN NAJERIYA – INJINIYA KAILANI

Yan Najeriya Su Yi Hankali Da Masu Son Zuciya

Daga Imrana Abdullahi

Gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu da suka hadu a karkashin kungiyar (Confederation of all APC support group) da suka yi fafutukar ganin jam’iyyar APC ta samu nasara sun yi kira ga shugabannin addinai a ko’ina suke da su yi hankali da irin kalaman da suke furtawa game da shugabancin Najeriya da harkokin siyasa baki daya.

Darakta Janar na gamayyar  kungiyoyin Injiniya Dokta Kailani Muhammad ne ya yi wannan kiran a wajen wani taron manema labarai da ya kira a Kaduna.

Injiniya Kailani ya ce hakika duk da irin yanayin halin tattalin arzikin da ake ciki Najeriya na ci gaba a halin yanzu, duk da cewa mutane na yin korafe – korafe a game da batun cire tallafin Man fetur.

” Ya dace jama’a su Sani fa cewa wannan Gwannatin karkashin shugaba Bola Ahmad Tinubu, ba ta wuce watanni biyu zuwa na uku ba , kuma da akwai shirye – shiryen da aka Sanya a gaba da aka yi kyakkyawan tsari da za a yi da nufin samar da saukin radadin wannan batu na tallafin Mai. Wanda kuma mun Sani cewa jama’a na cikin tsanani kwarai amma duk da haka idan aka yi duba tsakanin Najeriya, Benin da Chadi da sauran kasashen Afrika muna sayar da fetur a farashin da ke da sauki kwarai ba kamar su ba, shugaban kasa ya na kokari kwarai da gaske domin ya rigaya ya samar da tsaro sosai. Da akwai taimakon gaggawa a kan batun Noma, akwai kuma batun samun dai- daito a kan farashi da nufin samun tssyayyen farashi ba kamar yadda kowa ke yin abin da ya ga dama ba da sunan farashin kayan da yake Sayarwa. Saboda haka ni ina son in gaya wa jama’a cewa wannan tsarin ana bin sa ne a hankali kuma kamar yadda muke shaida maku cewa lallai zai haifar da nasara a nan gaba kadan”, Inji Dokta Kailani.

Saboda haka ne muke cewa jama’a ya dace su Sani cewa dole ne sai an yi sadaukarwa, kuma ai kamar yadda suke fadin cewa abin da ake samu a yanzu na kudin da aka cire tallafi kashi 25 zai je ne a harkar ilimi kashi 15 mata da kananan yara ga kuma bayar da tallafin karatu ga kuma batun harkar tsaro na musamman da kuma wadanda ake da su tun da dadewa, duk da mun san cewa lamarin zai dauki lokaci amma dai muna son yan Najeriya su ba Gwannatin nan cikakken hadin kai da goyon baya domin a yanzu babu maganar yin abin da aka saba a  kamar yadda aka saba tun can baya”.

” Muna yin kira ga yan Najeriya da su bayar da cikakken hadin kai da goyon baya a kuma ba Gwannati lokaci wadatacce domin aiwatar da ayyukan ciyar da kasa da al’ummarta gaba”.

Sai dai Dokta Kailani ya fadakar da jama’a cewa kada  yan kungiyar Kwadago su sake har yan a fasa kowa ya rasa su samu nasara a kansu domin akwai wadansu masu muguwar boyayyar manufa da suke a koda yaushe suna kokarin samun biyan bukatun kansu ne musamman ma idan aka yi la’akari da idan an haifar da yaki a kowa ce kasa a duniya , saboda haka muke ganin ya dace lallai mu hadu wuri daya da nufin goyon bayan Gwamnati mai ci a yanzu domin abubuwa su ta fi kamar yadda ya dace saboda mu muna da masaniyar cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya na aiki tukuru domin a fita daga cikin halin da ake ciki”.

Injiniya Dokta Kailani Muhammad ya ci gaba da bayanin cewa a game da kalaman da wani Malamin addinin Kirista ya yi cewa wai Tinubu bai ci zabe ba duk wannan shafi fadi ne kawai domin ya na batun son zuciyarsa ne kawai.

Akwai misali ” ko a zamanin Shehu Shagari sai da Awolowo ya kai shi kasa cewa wai bai ci zaben Abuja ba don haka kotun ta yanke hukuncin cewa wannan bai kai dalilin da za a ce Shagari bai ci zabe ba. Saboda haka muna sane a fili cewa Bola Ahmed Tinubu ya samu kashi Ashirin da biyar a  Jihohi a kalla 24 zuwa da shida wanda kuma ya kai mizanin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar. Kuma ina ganin shi wannan mutumin da ke wadannan kalaman ai bayarabe ne kuma shi ma shugaban kasa na yanzu Bola Tinubu ma Bayarabe ne amma kuma sai suka kawai wancan mutumin da ya kasance Bayerabe kawai yake ta yi duk da haka mu ba mu damu ba saboda sama da kashi Tamanin na al’ummar Yarbawa ba su zabi Tinubu ba suk da kungiyar Afenifere ta Yarbawa zalla duk ba su zabi Tinubu ba. Haka kuma irin su Tunde Bakare ma da sauransu duk sun ce ba su san shi. Saboda haka ne muke gayawa jama’a cewa babu wanda ya Isa ya cire Tinubu sai Allah kawai, domin yan Najeriya ne suka zabe shi kuma yan kasa sun yi magana ta hanyar kuri’a”.

Wai har shi wannan Malamin addinin Kiristan na cewa ba a kammala zabe ba don haka bai kare ba. Amma dai mun san cewa alkalan nan dai za su yi abin da ya dace a koda yaushe kuma a lokacin da ya dace, bari in gaya maku ku yan jarida abin da jam’iyyun Lebo da PDP keda shi a kotu shi ne ba wasu hujjojin alkalumma ba ne domin ya dace a shaida mana cewa mazabu dubu 148900 da ake da su cewa an samu matsala ko dai ta karya ka’idar yin zabe ko inda wasu mutane ke sace akwatin zabe su gudu da shi ko kuma inda aka cike akwatunan Zabe da kuri’un Bogi, amma duk ba su fadi hakan ba kawai abin da suke cewa shi ne Abuja – Abuja Abuja kawai cewa shugaban kasa bai ci zaben Abuja ba sun mance cewa shugaban kasa ya samu kashi biyu cikin uku na yawan kuri’un da aka kada kuma ya samu kashi 24 zuwa da shida na Jihohi kamar yadda doka ta tanadar.

Kuma a shekarar 1979 ma ai an yi hakan a tsakanin Awolowo da Shagari inda kotu da yi watsi da karar Awolowo domin kawai suna ta ambatar Abuja sai kotu ta ce a’a, hakan ba shi a cikin kundin tsarin mulki sai dan takara ya ci zabe a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja bayan kuma shugaba kasa ya lashe zabe a Jihohi sama da 25. Saboda haka ne muke yin kira ga daukacin yan Najeriya da kasa su goyi bayan wannan yunkurin da wasu ke yi . Kuma muna son ma jami’an tsaro su kama shi domin hakan zai iya kawo yaki kasancewarsa shi shugaban ne a wani Coci a Najeriya.

Kuma “muna yin kira ga John Onayekan da ya zo ya shigo cikin harkokin siyasa domin ya ga irin yadda ake yin siyasa, amma ba kawai mutum na zaune a cikin gidansa a shararren wuri ba sai wasu su rika yin amfani da shi domin kawai a haifar da matsalar lalata al’amura don haka muke kara ankarar da jami’an tsaro da kada su dauki lamarin da sauki ko saki- Sako”, Inji Dokta Kailani Muhammad.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.