Home / Big News / Bello Muhammad Zaki Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP zuwa ADC A Jigawa

Bello Muhammad Zaki Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP zuwa ADC A Jigawa

 

 

Daga Imrana Abdullahi

Fitaccen Dan Jarida kuma Wanda ya yi wa tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, Sakataren yada labarai Kwamared Bello Muhammad Zaki, ya bayyana ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar ADC a Jihar Jigawa.

Bello Muhammad Zaki ya dai bayyana hakan ne a cikin wata takardar da ya aikewa shugabancin mazabarsa ta Unguwar Gabas da ke cikin garin Kazaure inda Yake tabbatar masu da ficewarsa daga cikin NNPP zuwa ADC.

GA Takardar nan da Bello Muhammad Zaki Ya rubutawa jam’iyyarsa

A cikin wannan takardar dai da ya aikewa NNPP ya hada har da katinsa na Zama Dan jam’iyyar NNPP a da can baya duk ya hada ya mayar wa jam’iyyar domin a samu tabbacin hakan kamar yadda ka’idar ta tanadar.

A cikin takardar da ya aikewa Jam’iyyar dai ya yi fatan alkairi ga tsohuwar Jam’iyyar tasa tare da mambobinta da kuma fatan a Shiga sabuwar shekara lafiya

About andiya

Check Also

Dangote headlines 2026 Gateway Trade Fair as Gov Abiodun hails Group for boosting Ogun’s Industrial Competitiveness

Ogun State Government has lauded the roles being played by the Pan-Africa conglomerate, Dangote Industries …

Leave a Reply

Your email address will not be published.