Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin Shugaba Muhammadu Buhari na ganin al’amura sun inganta a fadin tarayyar Najeriya ya sauke ministoci biyu na ma’aikatun Noma Sabo Nanono da kuma na Lantarki Sale Mamman.
Bayanin hakan na kunshe na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriya, Femi Adesina ya fitar a wannan Larabar.
Sanarwar ta ce Ministan Muhalli, Mohammed Abubakar ne zai maye gurbin Ministan Noma, yayinda karamin Ministan ayyuka, Abubakar Aliyu zai maye gurbin Ministan Lantarki, fata dai Allah ya fitar da kasar cikin halin da ta shiga ya kuma taimakawa masu samun ci gaba a koda yaushe.