Home / Big News / Cibiyar Tabbatar Da Ci Gaban Dimokuraɗiyya CDD Ta Horar Da Yan Jarida A Kaduna

Cibiyar Tabbatar Da Ci Gaban Dimokuraɗiyya CDD Ta Horar Da Yan Jarida A Kaduna

Daga Imrana Abdullahi
Mista Peter Yohanna jami’i ne da ke aiki a Cibiyar tabbatar da ci gaba da bunkasa Dimokuraɗiyya ta CDD ya bayyana makasudin da ya sa suka zo Kaduna domin horas da yan jarida inda ya ce sun zo ne domin fadakarwa a game da irin yadda ya da ce yan jarida su tace labarai kafin yada su ga jama’a.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron da aka yi a Otal din Stone hedge a cikin garin Kaduna.
Yohanna ya ci gaba da bayanin cewa a wadansu lokuta hakika ya na da matuƙar amfani a samu horas da yan jarida a kai a kai domin tunasar da su abubuwan da ke faruwa a duniyar yada labarai musamman a tsari irin na Dimokuraɗiyya.
Yohanna ya ce makasudin zuwansu Kaduna shi ne a horas da yan jarida a kan batun gudanar da bincike da tantance bayanai kafin yada su ga jama’a wanda Abu ne mai matukar muhimmanci kwarai.
“Akwai labarai da yawa a kullum don haka a rika tantance su ta hanyar da ya dace kafin yada su har ma a wasu lokutan ba zaka iya gane wanene gaskiya wane labarin ne gaskiya ba don haka yi wa yan jarida horas wa abu ne mai kyau, shi ya sa muka horas da yan jarida idan sun ga labari su san wane ne gaskiya wane ne ba gaskiya ba ta yadda al’umma baki daya za ta amfani a cimma bukatar da kowa ke son a cimma ta tabbatar da gaskiya a hanyar labaran da ake haɗawa.
A wajen wannan taron dai an samu halartar manema labarai da yawa da suka hada daga kafafen labarai na rediyo,Talabijin,Jaridun buga wa natakardu da kuma na zamani da ake samun su a yanar Gizo da ake kira ( online).
Da wakilin mu ya ji ta bakin wasu mahalarta wannan taron horas wa yan jaridu da dama da wakilin mu ya tattauna da su sun bayyana jin dadinsu sakamakon gamsuwar da suka yi da taron horas War inda suka jinjinawa wannan Cibiya ta CDD da suka taso tun daga Abuja babban birnin tarayyar Najeriya suka zo Kaduna domin horas da yan jarida, abin da suka bayyana da cewa ci gaban kasa ne baki daya.

About andiya

Check Also

Why Yakubu Dogara Is Claiming Nigeria Is On The Right Track

By Imrana Abdullahi Nigeria is drowning while Rt. Hon. Yakubu Dogara smiles from the comfort …

Leave a Reply

Your email address will not be published.