Home / Labarai / Cire Tallafin Mai: Mun Ajiye Tiriliyan Daya – Tinubu

Cire Tallafin Mai: Mun Ajiye Tiriliyan Daya – Tinubu

Daga Imrana Abdullahi

 Shugaba Bola Ahmed  Tinubu ya bayuana cewa gwamnatin tarayya da ta cire tallafin man fetur ta samu nasarar samun kudi  sama da Naira tiriliyan 1.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wani jawabi da aka watsa a fadin kasar a daren ranar Litinin.

Ya ce kudaden, wadanda idan ba haka ba, da sun tafi harkar da ba ta da amfani, yanzu za a yi amfani da su wajen ganin an samu saukin ilimi ga ‘yan Najeriya.

“A cikin sama da  watanni biyu, mun yi tanadin sama da Naira tiriliyan da za a yi barna a kan tallafin man fetur da ba a samar da shi ba wanda kawai masu fasa-kwauri da masu damfara suke amfana a can baya.

“Wadannan kuɗin za a yi amfani da su kai tsaye kuma mafi amfani gare ku da danginku,  Misali, za mu cika alkawarinmu na sanya ilimi ya fi araha ga kowa da kuma ba da lamuni ga daliban da za su iya bukata.

“Babu wani dalibi dan Najeriya da zai bar karatun boko saboda rashin kudi.

Alƙawarinmu shi ne inganta mafi girman alheri ga mafi yawan mutanenmu.  A kan wannan ka’ida, ba za mu taba yin kasala ba,” in ji shi.

Ya kara da cewa tuni gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da kungiyoyin kwadago domin gabatar da sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa.

“Da zarar mun amince da sabon mafi karancin albashi da kuma sake dubawa na gaba daya, za mu yi tanadin kasafin kudin don aiwatarwa cikin gaggawa,” in ji shi.

Shugaban ya kuma yabawa ma’aikata masu zaman kansu a cikin kamfanoni masu zaman kansu waɗanda suka riga sun aiwatar da bitar albashi na gabaɗaya ga ma’aikata.

A cewarsa, gwamnati na kokarin ganin ta dinke barakar da ake samu domin moriyar jama’a.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya na hada hannu da jahohi da kananan hukumomi domin aiwatar da ayyukan da za su dakile illar korar jama’a.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.