Home / KUNGIYOYI / A Sama Wa Direbobi Hanyoyin Samun Sauki – Aliyu Tanimu Zariya

A Sama Wa Direbobi Hanyoyin Samun Sauki – Aliyu Tanimu Zariya

Muna Faduwa A Sana’ar Tuki

Daga Imrana Abdullahi

An yi kira ga Gwamnati da ta samar wa daukacin direbobi masu sana’ar tukin mota da hanyoyin samun saukin radadin cire tallafin Man fetur ta yadda rayuwar kowa za ta inganta.

Alhaji Aliyu Tanimu Zariya, shugaba ne na kungiyar Direbobi ta kasa (NURTW) reshen Jihar Kaduna ya yi wannan kiran ga Gwannati a lokacin da ya tattauna da wakilin mu a Kaduna.

Tanimu Aliyu Zariya ya ce kamar kowace irin sana’a da kuma kasuwanci suma direbobi duk suna zuba kudinsu ne su yi sana’ar tukin mota domin su rufawa kai da iyalai da yan uwa asiri.

” Amma a yanayin da aka samu kai game da batun cire tallafin mai hakika lamarin ya Jefa direbobin mota cikin wani mawuyacin hali inda har sun kai ga wasu da yawa a cikin direbobin sun ajiye motocin da suke neman abincin da su”.

Tanimu Zariya ya ci gaba da bayanin lamarin karin Man fetur din nan ba wanda ya shafa kamar direbobi saboda sana’ar mu sai da Mai ya zama wajibi sai da Mai dole, kuma a kullum dan Adam na kokarin duba wace hanya ce mafita ga sana’ar da yake yi kamar kudi ne a hannun mutum ka juya su ka san meye riba kuma yaya zai yi duk domin ya samu ci gaba , haka sana’ar mota take idan mutum na da mota ya sayi Mai ya na sa ran cin riba ne, misali idan direba ya sayi Man dubu Goma ai ya na saran samun dubu Goma sha uku koma sha Biyar idan ya dauki fasinjoji. A yanayin wannan karin kudin man da aka yi ya ninka dole kungiyar direbobi da direbobi su san meye mafita duk da yanayin da ake ciki na ba kudi a hann8n mutane. Sannan wani abu ma mutanen ba su iya fitowa domin su hau mota, amma duk da hakan direbobi ke yin kokarin aiwatar da aikin a yadda ya samu”, inji Tanimu Zariya.

Ya tabbatar da cewa akwai babban korafin direbobi shi ne na faduwa a sana’ar tukin da muke yi ” domin a yanzu ya kasance direbobi na yin sana’ar me babu riba, misali kamar direba ne ya zuba Mai a motarsa ya ta fi Zariya idan yaje da fasinja idan ya dawo ba fasinja hakika ya fadi saboda haka nan da Zariya sai kaga direba idan yaje sai kaga ya tsaya ya kwana domin jiran lodi? amma a lokacin da mai na sauki direba zai iya zuwa Zariya daga Kaduna ya dawo sau uku ko hudu a rana daya yanzu kuwa ba zai yuwu ba saboda da ka bi hanyar ba ma fadinjan da zaka dauka in kuma ka koma mai hakika ka kona kudi mai yawa saboda haka dole ne direba ya rika yin korafin halin da ya samu kansa a ciki. Wasu ma sun ajiye Motocinsu suna jiran su ga yadda lamarin zai kaya sai dai kawai wasu masu dauriya kawai haka nan da dafi  ba dadi haka kawai ake yin abin”.

” Duk da cewa a lokacin Yakin neman zabe ana ta neman jama’a ne da yi wa kowa alkawari duk da hakan ba za a ce lokacin cika alkawari ya yi ko bai yi ba saboda a yanzu ne ake kokarin kafa Gwamnatin baki daya don haka muna dai zura idanu muga me zai faru, muna cikin wadanda suka yi uzuri ga Gwamnati.

Ga Tanimu Aliyu Zariya nan da yayansa masa guda biyu tare da mambobin kungiyar NURTW reshen Jihar Kaduna a wannan hoton

Saboda haka ni a matsayina ina yin kira ga Gwamnati da ta duba irin halin da direbobi ke ciki domin duba wata hanyar da za a samar mana da sassauci wajen sana’ar mu ta tukin mota. Kuma haka nan Gwannatin ta duba a cikin al’umma nan ma wane tallafin za ta yi domin kowa ya samu sauki a kan irin wannan saboda halin da ake ciki na tsadar mai ya shafi kowa har ya shaddada kwarai. Kamar a can baya direbobi na alfaharin cewa suna da sana’a amma suma a yanzu suna ajiye motocin domin ba yadda za su yi har suna neman shiga layin masu zama haka nan tun da jama’a ba su fito ba domin su dauke su.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.