Home / Lafiya / Cutar Korona: Gwamnan Bauchi Ya Killace Kansa

Cutar Korona: Gwamnan Bauchi Ya Killace Kansa

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammed ya killace kansa saboda tsoron ko ya kamu da cutar Covid 19 da ake Kira Korona Birus.

Bayanin hakan dai ya faru ne sakamakon irin cudanyar da Gwamna tare da wadansu daga cikin mutanen da suke tare da shi suka gaisa da tattaunawa hadi da shiga Jirgi daya da Dan Atiku Abubalar da ya shelantawa duniya cewa ya kamu da cutar korona

Da yake bayanin hakan a shafinsa na tuwita shugaban ma’aikatan gidan Gwamnatin Jihar Bauchi Malam Ladan Salihu cewa ya yi hakika mun hadu da shi lokacin da muka shiga cikin Jirgi daya daga Legas zuwa Abuja.

Ya ce ” Gwamnan mu Bala Muhammed ya killace kansa saboda ya hadu da Dan Atiku Abubakar.

“Hakika gaskiya ne muna cikin Jirgi daya daga Legas zuwa Abuja. Sun kuma gaisa mun kuma tattauna.

“Gwamnan tare da wadansunmu mun yi Gwaji kuma da yardar Allah komai lafiya kalau.

About andiya

Check Also

An Rantsar Da Ishaya Idi Sabon Shugaban Kasuwar Duniya Ta Kaduna

  Daga Imrana Abdullahi A kokarin ganin al’amura sun ci gaba da tafiya kamar yadda …

Leave a Reply

Your email address will not be published.